< Revelation 15 >

1 I saw another great and marvelous sign in the sky: seven angels having the seven last plagues, for in them God’s wrath is finished.
Na ga wata babbar alama mai banmamaki a sama, mala’iku bakwai da annobai bakwai na ƙarshe, na ƙarshe, domin da su ne fushin Allah ya cika.
2 I saw something like a sea of glass mixed with fire, and those who overcame the beast, his image, and the number of his name, standing on the sea of glass, having harps of God.
Sai na ga abin da ya yi kamar tekun gilashi gauraye da wuta kuma tsaye kusa da teku, waɗanda suka ci nasara bisan dabbar da siffarta da bisan lambar sunanta. Suna riƙe da garayu waɗanda Allah ya ba su
3 They sang the song of Moses, the servant of God, and the song of the Lamb, saying, “Great and marvelous are your works, Lord God, the Almighty! Righteous and true are your ways, you King of the nations.
suka rera waƙar Musa bawan Allah da kuma waƙar Ɗan Ragon suna cewa, “Ayyukanka suna da girma da kuma banmamaki, ya Ubangiji Maɗaukaki. Al’amuranka suna da aminci da kuma gaskiya, ya Sarkin zamanai.
4 Who wouldn’t fear you, Lord, and glorify your name? For you only are holy. For all the nations will come and worship before you. For your righteous acts have been revealed.”
Wane ne ba zai ji tsoronka, yă kuma kawo ɗaukaka ga sunanka ba, ya Ubangiji? Gama kai kaɗai ne mai tsarki. Dukan al’ummai za su zo su yi sujada a gabanka, gama an bayyana ayyukan adalcinka.”
5 After these things I looked, and the temple of the tabernacle of the testimony in heaven was opened.
Bayan wannan sai na duba, a cikin sama kuwa sai ga haikali, wato, tabanakul na Shaida, a buɗe.
6 The seven angels who had the seven plagues came out, clothed with pure, bright linen, and wearing golden sashes around their chests.
Daga cikin haikalin mala’iku bakwai tare da annobai bakwai suka fito. Suna saye da tufafin lilin masu tsabta masu walƙiya, suna kuma saye da ɗamarar zinariya a ƙirjinsu.
7 One of the four living creatures gave to the seven angels seven golden bowls full of the wrath of God, who lives forever and ever. (aiōn g165)
Sai ɗaya daga cikin halittu huɗun nan masu rai, ya ba wa mala’iku bakwai nan kwanonin zinariya bakwai cike da fushin Allah, wanda yake raye har abada abadin. (aiōn g165)
8 The temple was filled with smoke from the glory of God and from his power. No one was able to enter into the temple until the seven plagues of the seven angels would be finished.
Aka kuma cika haikalin da hayaƙi daga ɗaukakar Allah da kuma daga ikonsa, kuma ba wanda ya iya shiga haikalin sai da aka cika annobai bakwai nan na mala’iku bakwai.

< Revelation 15 >