< Malachi 1 >

1 A revelation, Yahweh’s word to Israel by Malachi.
Annabci, wannan ita ce maganar Ubangiji ga Isra’ila ta wurin Malaki.
2 “I have loved you,” says Yahweh. Yet you say, “How have you loved us?” “Wasn’t Esau Jacob’s brother?” says Yahweh, “Yet I loved Jacob;
“Na ƙaunace ku, in ji Ubangiji. “Amma sai kuka ce, ‘Yaya ka ƙaunace mu?’ “Isuwa ba ɗan’uwan Yaƙub ba ne?” In ji Ubangiji. “Duk da haka na ƙaunaci Yaƙub,
3 but Esau I hated, and made his mountains a desolation, and gave his heritage to the jackals of the wilderness.”
amma na ƙi Isuwa, na kuma mai da ƙasarsa da take kan duwatsu kango, na ba da gādonsa ga dilolin hamada.”
4 Whereas Edom says, “We are beaten down, but we will return and build the waste places,” Yahweh of Armies says, “They shall build, but I will throw down; and men will call them ‘The Wicked Land,’ even the people against whom Yahweh shows wrath forever.”
Edom zai iya cewa, “Ko da yake an ragargaza mu, ai, za mu sāke gina kufanmu.” Amma ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Za su iya gini, amma zan rushe. Za a ce da su Muguwar Ƙasa, mutane da kullum suke a ƙarƙashi fushin Ubangiji.
5 Your eyes will see, and you will say, “Yahweh is great—even beyond the border of Israel!”
Za ku ga wannan da idanunku ku kuma ce, ‘Ubangiji da girma yake, har gaba da iyakokin Isra’ila ma!’
6 “A son honors his father, and a servant his master. If I am a father, then where is my honor? And if I am a master, where is the respect due me?” says Yahweh of Armies to you priests who despise my name. “You say, ‘How have we despised your name?’
“Ɗa yakan girmama mahaifinsa, bawa kuma yakan girmama maigidansa. In ni mahaifi ne, ina girman da ya dace da ni? In ni maigida ne, ina girman da ya dace da ni?” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “Ku firistoci, ku ne kuka rena sunana. “Amma sai kuka ce, ‘Yaya muka rena sunanka?’
7 You offer polluted bread on my altar. You say, ‘How have we polluted you?’ In that you say, ‘Yahweh’s table is contemptible.’
“Kun ajiye abinci mai ƙazanta a kan bagadena. “Sai kuka ce, ‘Yaya muka ƙazantar da kai?’ “Ta wurin cewa teburin Ubangiji abin reni ne.
8 When you offer the blind for sacrifice, isn’t that evil? And when you offer the lame and sick, isn’t that evil? Present it now to your governor! Will he be pleased with you? Or will he accept your person?” says Yahweh of Armies.
Sa’ad da kuka kawo makauniyar dabba don ku miƙa mini hadaya, wannan daidai ne? Sa’ad da kuka miƙa gurguwar dabba ko marar lafiya, wannan daidai ne? Ku gwada ba wa gwamnanku irin wannan ku gani! Kuna gani zai ji daɗinku? Zai karɓe ku ne?” In ji Ubangiji Maɗaukaki.
9 “Now, please entreat the favor of God, that he may be gracious to us. With this, will he accept any of you?” says Yahweh of Armies.
“To, firistoci yanzu ku gwada ku roƙi Allah yă yi mana alheri. Da irin hadayun nan a hannuwanku ne zai ji ku?” In ji Ubangiji Maɗaukaki.
10 “Oh that there were one among you who would shut the doors, that you might not kindle fire on my altar in vain! I have no pleasure in you,” says Yahweh of Armies, “neither will I accept an offering at your hand.
“Kash, da ma wani daga cikinku ya rufe ƙofofin haikali don kada ku shiga, ku hura wuta marar amfani a bisa bagadena! Ba na jin daɗinku, ba zan kuwa karɓi hadaya daga hannuwanku ba” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
11 For from the rising of the sun even to its going down, my name is great among the nations, and in every place incense will be offered to my name, and a pure offering; for my name is great among the nations,” says Yahweh of Armies.
Sunana zai zama mai girma a cikin al’ummai, daga fitowar rana har zuwa fāɗuwarta. A kowane wuri za a miƙa wa sunana turare da tsabtacciyar hadaya domin sunana zai zama mai girma a cikin al’ummai, in ji Ubangiji Maɗaukaki.
12 “But you profane it when you say, ‘Yahweh’s table is polluted, and its fruit, even its food, is contemptible.’
“Amma kun ƙazantar da sunana ta wurin cewa ‘Teburin Ubangiji ya ƙazantu,’ kuka kuma yi magana a kan abincinsa kuna cewa, ‘Abin reni ne.’
13 You say also, ‘Behold, what a weariness it is!’ And you have sniffed at it”, says Yahweh of Armies; “and you have brought that which was taken by violence, the lame, and the sick; thus you bring the offering. Should I accept this at your hand?” says Yahweh.
Kun kuma ce, ‘Mun gaji da irin wannan wahala!’ Kuna hura mini hancin reni,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Sa’ad da kuka kawo raunannu, gurguntattun dabbobi, ko kuma dabbobi masu fama da cuta, kuka kuma miƙa su hadaya, kuna gani zan karɓi wannan daga gare ku?” In ji Ubangiji.
14 “But the deceiver is cursed who has in his flock a male, and vows and sacrifices to the Lord a defective thing; for I am a great King,” says Yahweh of Armies, “and my name is awesome among the nations.”
“La’ananne ne macucin da yake da lafiyayyiyar dabba namiji a garkensa wadda ya yi alkawari zai bayar, amma sai ya miƙa hadayar dabba mai aibi ga Ubangiji. Gama ni babban sarki ne, za a kuma ji tsoron sunana a cikin al’ummai,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

< Malachi 1 >