< Luke 7 >

1 After he had finished speaking in the hearing of the people, he entered into Capernaum.
Bayan da Yesu ya gama fadar dukan abubuwan da zai fadi a jin kunnen dukan mutanen, sai ya shiga Kafarnahum.
2 A certain centurion’s servant, who was dear to him, was sick and at the point of death.
Bawan wani jarumi, wanda yake kauna, ba shi da lafiya har ma ya kusa mutuwa.
3 When he heard about Jesus, he sent to him elders of the Jews, asking him to come and save his servant.
Amma da ya ji labarin Yesu, jarumin ya aiki wadansu dattawan Yahudawa, ya ce a roki Yesu ya zo ya ceci bawansa daga mutuwa.
4 When they came to Jesus, they begged him earnestly, saying, “He is worthy for you to do this for him,
Sa'adda su ka zo kusa da Yesu, su ka roke shi da gaske, cewa, “Wannan ya isa ka yi masa haka,
5 for he loves our nation, and he built our synagogue for us.”
saboda shi mai kaunar kasar mu ne, kuma shi ne ya gina mana majami'a.
6 Jesus went with them. When he was now not far from the house, the centurion sent friends to him, saying to him, “Lord, don’t trouble yourself, for I am not worthy for you to come under my roof.
Sai Yesu ya tafi tare da su. Amma sa'adda ya zo kusa da gidan mutumin, jarumin ya aiki abokansa su ka ce da shi, “Ubangiji kada ka damu domin ni ban isa ka zo gida na ba.
7 Therefore I didn’t even think myself worthy to come to you; but say the word, and my servant will be healed.
Shi ya sa na ga ban isa in zo wurinka ba, ka yi magana kadai bawa na kuwa zai warke.
8 For I also am a man placed under authority, having under myself soldiers. I tell this one, ‘Go!’ and he goes; and to another, ‘Come!’ and he comes; and to my servant, ‘Do this,’ and he does it.”
Gama ni ma mutum ne mai iko, ina da sojoji karkashina. Ina iya cewa da wannan, 'Ka je' sai ya tafi, in kuma ce da wani 'ka zo' sai ya zo, in kuma ce da bawa na, 'Yi kaza,' sai ya yi.”
9 When Jesus heard these things, he marveled at him, and turned and said to the multitude who followed him, “I tell you, I have not found such great faith, no, not in Israel.”
Sa'adda Yesu ya ji haka, ya yi mamakin mutumin, ya juya wajen taron da su ke biye da shi, ya ce, “Na gaya maku, ko a cikin Isra'ila ban sami wani mai bangaskiya irin wannan ba”
10 Those who were sent, returning to the house, found that the servant who had been sick was well.
Daga nan wadanda a ka aika, suka dawo gida suka tarar da bawan cikin koshin lafiya.
11 Soon afterwards, he went to a city called Nain. Many of his disciples, along with a great multitude, went with him.
Wani lokaci bayan wannan, ya zama Yesu yana tafiya wani gari da ake kira Na'im. Almajiransa su na tare da shi, da kuma taron mutane masu yawa.
12 Now when he came near to the gate of the city, behold, one who was dead was carried out, the only born son of his mother, and she was a widow. Many people of the city were with her.
Sa'adda ya kusa da kofar garin, sai ga wani matacce ana dauke da shi. Kuma shi kadai ne da a wurin mahaifiyarsa. Ita kuwa gwauruwa ce, mutane da dama daga cikin gari suna tare da ita.
13 When the Lord saw her, he had compassion on her and said to her, “Don’t cry.”
Da ganin ta, sai Ubangiji ya cika da tausayi a game da ita ya ce da ita, “Kada ki yi kuka.”
14 He came near and touched the coffin, and the bearers stood still. He said, “Young man, I tell you, arise!”
Sai ya zo ya taba makarar, sai masu dauke da shi su ka tsaya. Ya ce 'Saurayi na ce ma ka ka tashi.”
15 He who was dead sat up and began to speak. Then he gave him to his mother.
Sai mataccen ya tashi ya fara yin magana. Sai Yesu ya ba mahaifiyar danta.
16 Fear took hold of all, and they glorified God, saying, “A great prophet has arisen among us!” and, “God has visited his people!”
Sai tsoro ya kama su duka. Su ka kama yabon Allah, su na cewa, “An ta da wani annabi mai girma a cikinmu” kuma “Allah ya dubi mutanensa.”
17 This report went out concerning him in the whole of Judea and in all the surrounding region.
Wannan labari na Yesu, ya ba zu a cikin dukan Yahudiya da yankuna da su ke kewaye.
18 The disciples of John told him about all these things.
Almajiran Yahaya suka gaya masa dukan wadannan abubuwa.
19 John, calling to himself two of his disciples, sent them to Jesus, saying, “Are you the one who is coming, or should we look for another?”
Sai Yahaya ya kira biyu daga cikin almajiransa, ya aike su wurin Ubangiji, suka ce da shi, “Kai ne mai zuwan nan, ko akwai wani wanda za mu saurari zuwansa?”
20 When the men had come to him, they said, “John the Baptizer has sent us to you, saying, ‘Are you he who comes, or should we look for another?’”
Sa'adda suka zo kusa da Yesu, sai mutanen suka ce, “Yahaya Mai Baftisma, ya aiko mu, mu tambaya, “Kai ne mai zuwan nan, ko akwai wani wanda za mu saurari zuwansa?”
21 In that hour he cured many of diseases and plagues and evil spirits; and to many who were blind he gave sight.
A cikin wannan lokaci, ya warkar da mutane da yawa daga cututtuka da matsaloli da miyagun ruhohi. Makafi da yawa sun sami ganin gari.
22 Jesus answered them, “Go and tell John the things which you have seen and heard: that the blind receive their sight, the lame walk, the lepers are cleansed, the deaf hear, the dead are raised up, and the poor have good news preached to them.
Yesu, ya amsa ya ce masu, “Bayan kun tafi, ku ba Yohanna rahoton abin da ku ka ji da abin da ku ka gani. Makafi suna ganin gari, guragu suna tafiya, ana kuma tsarkake kutare. Kurame suna ji, ana tayar da matattu, ana gaya wa matalauta labari mai dadi.
23 Blessed is he who finds no occasion for stumbling in me.”
Mai albarka ne mutumin da ya tsaya a kan ba da gaskiya gare ni saboda ayukan da na ke yi.”
24 When John’s messengers had departed, he began to tell the multitudes about John, “What did you go out into the wilderness to see? A reed shaken by the wind?
Bayan da mutanen da Yahaya ya aiko suka tafi, Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yahaya. “Me ku ka tafi ku gani a cikin hamada, ciyawa wadda iska ta ke girgizawa?
25 But what did you go out to see? A man clothed in soft clothing? Behold, those who are gorgeously dressed and live delicately are in kings’ courts.
Amma me ku ka tafi domin ku gani, mutum mai saye da tufafi masu taushi? Duba mutanen da su ke saye da tufafi masu daraja, kuma suna rayuwa cikin jin dadi suna fadar sarakuna.
26 But what did you go out to see? A prophet? Yes, I tell you, and much more than a prophet.
Amma me ku ka tafi domin ku gani, annabi ne? I, ina gaya ma ku, ya ma fi annabi.
27 This is he of whom it is written, ‘Behold, I send my messenger before your face, who will prepare your way before you.’
Wannan shine wanda aka rubuta a kansa, “Duba, ina aika manzo na a gabanka, wanda za ya shirya maka hanya a gabanka.
28 “For I tell you, among those who are born of women there is not a greater prophet than John the Baptizer; yet he who is least in God’s Kingdom is greater than he.”
Ina gaya maku, a cikin wadanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yahaya girma. Duk da haka, wanda ya fi kankanta a mulkin Allah, ya fi shi girma.
29 When all the people and the tax collectors heard this, they declared God to be just, having been baptized with John’s baptism.
Sa'anda dukan mutane suka ji haka, har da ma su karbar haraji, suka shaida Allah mai adalci ne. Su na cikin wadanda Yahaya ya yi wa baftisma.
30 But the Pharisees and the lawyers rejected the counsel of God, not being baptized by him themselves.
Amma Farisawa da wadanda su ke kwararru a cikin shari'ar Yahudawa, wadanda ba shi ne ya yi masu baftisma ba, suka yi watsi da hikimar Allah don kansu.
31 “To what then should I compare the people of this generation? What are they like?
Sa'annan Yesu ya ce, “Da me zan kamanta mutanen wannan zamani? Da me suka yi kama?
32 They are like children who sit in the marketplace and call to one another, saying, ‘We piped to you, and you didn’t dance. We mourned, and you didn’t weep.’
Suna kama da yaran da suke wasa a kasuwa, wadanda suke magana da junansu suna cewa, “Mun yi maku busa, ba ku yi rawa ba. Mun yi makoki, ba ku yi kuka ba.”
33 For John the Baptizer came neither eating bread nor drinking wine, and you say, ‘He has a demon.’
Haka, Yahaya ya zo, bai ci gurasa ba, bai sha ruwan inabi ba, amma ku ka ce, 'Aljani ne yake mulkinsa.
34 The Son of Man has come eating and drinking, and you say, ‘Behold, a glutton and a drunkard, a friend of tax collectors and sinners!’
Dan Mutum, ya zo, yana ci, yana sha, amma, kuka ki shi, kuna cewa dubi mutum mai hadama, mai shan ruwan inabi da yawa, abokin masu karbar haraji da masu zunubi!
35 Wisdom is justified by all her children.”
Amma hikimar Allah tana shaidar dukan 'yayanta.”
36 One of the Pharisees invited him to eat with him. He entered into the Pharisee’s house and sat at the table.
Wata rana wani Bafarise, ya roki Yesu ya je ya ci abinci tare da shi. Bayan da Yesu ya shiga gidan Bafarisen, ya zauna a teburi domin ya ci abinci.
37 Behold, a woman in the city who was a sinner, when she knew that he was reclining in the Pharisee’s house, brought an alabaster jar of ointment.
Sai ga wata mace mai zunubi, ta fito daga cikin birni. Sa'anda ta ji labari Yesu yana gidan Bafarisen, domin ya ci abinci. Ta dauki tandun mai na alabastar mai kamshi.
38 Standing behind at his feet weeping, she began to wet his feet with her tears, and she wiped them with the hair of her head, kissed his feet, and anointed them with the ointment.
Ta tsaya kusa da Yesu tana kuka. Ta fara jika kafafunsa da hawayenta, tana shafe kafafunsa da gashin kanta. Tana yi wa kafafunsa sumba, tana shafe su da turare.
39 Now when the Pharisee who had invited him saw it, he said to himself, “This man, if he were a prophet, would have perceived who and what kind of woman this is who touches him, that she is a sinner.”
Sa'anda Bafarisen da ya gaiyaci Yesu, ya ga haka, sai ya yi tunani a cikin ransa, da cewa, “In da wannan mutum annabi ne, da ya gane ko wacce irin mace ce, wannan da take taba shi, ita mai zunubi ce.”
40 Jesus answered him, “Simon, I have something to tell you.” He said, “Teacher, say on.”
Yesu ya amsa ya ce masa, “Siman, ina so in gaya maka wani abu.” Ya ce, “malam sai ka fadi!”
41 “A certain lender had two debtors. The one owed five hundred denarii, and the other fifty.
Yesu ya ce, “wani mutum mai ba da bashi yana bin wadansu mutane su biyu kudi, yana bin dayan sule dari, dayan kuma yana bin sa sule hamsin.
42 When they couldn’t pay, he forgave them both. Which of them therefore will love him most?”
Da yake ba su da kudin da za su iya biyan sa, sai ya yafe masu, su duka biyu. A cikin su biyu, wanne ne zai fi nuna kauna ga wannan mutum?”
43 Simon answered, “He, I suppose, to whom he forgave the most.” He said to him, “You have judged correctly.”
Siman ya amsa ya ce, “Ina tsammani wanda ya yafe wa kudi da yawa.” Yesu ya amsa ya ce masa, “Ka shari'anta dai dai.”
44 Turning to the woman, he said to Simon, “Do you see this woman? I entered into your house, and you gave me no water for my feet, but she has wet my feet with her tears, and wiped them with the hair of her head.
Yesu ya juya wajen matar, ya ce da Siman, “Ka ga matan nan. Na shiga gidanka. Ba ka ba ni ruwa domin kafafuna ba, amma ita ta ba ni, da hawayenta ta wanke kafafuna, ta kuma shafe su da gashin kanta.
45 You gave me no kiss, but she, since the time I came in, has not ceased to kiss my feet.
Kai ba ka yi ma ni sumba ba, amma ita ta yi, tun sa'adda na shigo nan ba ta dena sumbatar kafafuna ba.
46 You didn’t anoint my head with oil, but she has anointed my feet with ointment.
Kai ba ka shafe kai na da mai ba, amma ita ta shafe kafafuna da turare.
47 Therefore I tell you, her sins, which are many, are forgiven, for she loved much. But one to whom little is forgiven, loves little.”
Saboda haka, ita wadda ta ke da zunubi da yawa ta bayar da mai yawa, ta kuma nuna kauna mai yawa. Amma shi wanda aka gafarta wa kadan, ya kuma nuna kauna kadan.”
48 He said to her, “Your sins are forgiven.”
Daga nan sai ya ce mata, “An gafarta zunubanki.”
49 Those who sat at the table with him began to say to themselves, “Who is this who even forgives sins?”
Wadanda su ke a nan zaune tare da shi suka fara magana da junansu, “Wanene wannan wanda har yake gafarta zunubai?
50 He said to the woman, “Your faith has saved you. Go in peace.”
Sai Yesu ya ce da matar, “Bangaskiyarki ta cece ki. Ki tafi da salama.”

< Luke 7 >