< Luke 15 >

1 Now all the tax collectors and sinners were coming close to him to hear him.
To sai duk masu karbar haraji da masu zunubi suna ta zuwa wurin Yesu suna sauraronsa.
2 The Pharisees and the scribes murmured, saying, “This man welcomes sinners, and eats with them.”
Dukan Farisawa da Marubuta suna ta gunaguni da junansu, cewa, “Wannan mutum yana karbar masu zunubi, har ma tare suke cin abinci.”
3 He told them this parable:
Yesu ya fadi wannan misali, ya ce,
4 “Which of you men, if you had one hundred sheep and lost one of them, wouldn’t leave the ninety-nine in the wilderness and go after the one that was lost, until he found it?
“Idan waninku yana da tumaki dari, sai dayarsu ta bace, wato ba zai bar tasa'in da taran nan a makiyaya, ya bi sawun wadda ta bata gudan nan har sai ya same shi ba?
5 When he has found it, he carries it on his shoulders, rejoicing.
Idan kuwa ya same ta, sai ya dauke ta a kafadarsa yana farin ciki.
6 When he comes home, he calls together his friends and his neighbors, saying to them, ‘Rejoice with me, for I have found my sheep which was lost!’
In ya dawo gida, sai ya kira abokansa da makwabta, yace masu, 'Ku taya ni murna don na samo tunkiyata da ta bata.'
7 I tell you that even so there will be more joy in heaven over one sinner who repents, than over ninety-nine righteous people who need no repentance.
Ina gaya maku, haka kuma za a yi farin ciki a sama, a kan mai zunubi guda da ya tuba, fiye da kan masu adalci tassa'in da tara wadanda ba su bukatar tuba.
8 “Or what woman, if she had ten drachma coins, if she lost one drachma coin, wouldn’t light a lamp, sweep the house, and seek diligently until she found it?
Ko kuwa wacce mace ce, in tana da kudi azurfa guda goma, in ta batar da daya, ba za ta kunna fitila ta share gidan, ta yi ta neman shi har sai ta same shi ba?
9 When she has found it, she calls together her friends and neighbors, saying, ‘Rejoice with me, for I have found the drachma which I had lost!’
In kuwa ta same shi sai ta tara kawayenta da makwabtanta, ta ce, 'Ku taya ni farin ciki don na sami kudin nan nawa da ya bace.'
10 Even so, I tell you, there is joy in the presence of the angels of God over one sinner repenting.”
Haka nake gaya maku, abin farin ciki ne ga mala'ikun Allah idan mai zunubi guda ya tuba.”
11 He said, “A certain man had two sons.
Sai Yesu ya ce, “Akwai wani mutum mai 'ya'ya biyu maza,
12 The younger of them said to his father, ‘Father, give me my share of your property.’ So he divided his livelihood between them.
sai karamin ya ce wa mahaifinsa, 'Baba, bani rabona daga cikin dukiyarka.' Sai mahaifinsa ya raba masu dukiyarsa tsakaninsu.
13 Not many days after, the younger son gathered all of this together and traveled into a far country. There he wasted his property with riotous living.
Bayan 'yan kwanaki kadan, sai karamin dan ya tattara duk mallakarsa, ya kama hanya zuwa wata kasa mai nisa. A can ya batas da kudinsa, yana sayan abubuwan da ba ya bukata, ya kuma batas da kudinsa a wajen masha'a.
14 When he had spent all of it, there arose a severe famine in that country, and he began to be in need.
Bayan da ya batas da duk abin da ya ke da shi, sai aka yi babbar yunwa a kasar, sai ya shiga fatara.
15 He went and joined himself to one of the citizens of that country, and he sent him into his fields to feed pigs.
Ya je ya mika kansa domin aiki ga wani dan kasar, sai ya aike shi cikin gonakinsa domin ya rika ba aladu abinci.
16 He wanted to fill his belly with the pods that the pigs ate, but no one gave him any.
Har yayi marmarin ya ci daga cikin barbashin da aladu suke ci, domin babu wanda yake ba shi wani abu ya ci.
17 But when he came to himself, he said, ‘How many hired servants of my father’s have bread enough to spare, and I’m dying with hunger!
Amma da hankalinsa ya dawo, ya ce, 'Barorin mahaifina su nawa ne da suke da abinci isasshe, amma ina nan a nan, ina mutuwa sabili da yunwa!
18 I will get up and go to my father, and will tell him, “Father, I have sinned against heaven and in your sight.
Zan tashi, in tafi gun mahaifina, in ce masa, “Baba, na yi wa sama zunubi, na kuma saba maka.
19 I am no more worthy to be called your son. Make me as one of your hired servants.”’
Ban cancanci a kara kira na danka ba; ka mai da ni kamar daya daga cikin barorinka.'”
20 “He arose and came to his father. But while he was still far off, his father saw him and was moved with compassion, and ran, fell on his neck, and kissed him.
Sai ya tashi, ya taho wurin mahaifinsa. Amma tun yana daga nesa, sai mahaifinsa ya hango shi tausayi ya kama shi, ya ruga a guje, ya rungume shi, ya yi ta sumbatar sa.
21 The son said to him, ‘Father, I have sinned against heaven and in your sight. I am no longer worthy to be called your son.’
Dan kuma ya ce masa, 'Baba, na yi wa sama zunubi, na kuma saba maka. Ban isa a kara kira na danka ba.'
22 “But the father said to his servants, ‘Bring out the best robe and put it on him. Put a ring on his hand and sandals on his feet.
Amma mahaifinsa ya ce wa bayinsa, 'Ku yi hamzari ku kawo riga mafi kyau, ku yafa masa. Ku sa masa zobe a hanunsa da takalma a kafafunsa.
23 Bring the fattened calf, kill it, and let’s eat and celebrate;
Sa'annan a kawo kiwataccen marakin nan, a yanka. Mu yi buki!
24 for this, my son, was dead and is alive again. He was lost and is found.’ Then they began to celebrate.
Gama da na ya mutu a da, amma yanzu yana a raye. Ya bata a da, amma a yanzu an same shi.' Sai suka fara liyafa.
25 “Now his elder son was in the field. As he came near to the house, he heard music and dancing.
A wannan lokacin, babban dansa yana gona. Da ya kai kusa da gida, ya ji ana kade-kade da raye-raye.
26 He called one of the servants to him and asked what was going on.
Sai ya kira wani bawan gidan, ya tambayi manufar wadannan abubuwa.
27 He said to him, ‘Your brother has come, and your father has killed the fattened calf, because he has received him back safe and healthy.’
Bawan ya ce masa, 'Dan'uwanka ne ya dawo gida, mahaifinka kuma ya yanka kiwataccen marakin nan, saboda ya dawo gida lafiya.'
28 But he was angry and would not go in. Therefore his father came out and begged him.
Amma dan'uwan ya yi fushi, ya ki ya shiga ciki, mahaifinsa kuwa ya fito, ya roke shi.
29 But he answered his father, ‘Behold, these many years I have served you, and I never disobeyed a commandment of yours, but you never gave me a goat, that I might celebrate with my friends.
Amma babban dan ya amsa wa ubansa ya ce, 'Duba, duk yawan shekarun nan da nake bauta maka, ban taba karya umarnin ka ba, duk da haka ba ka taba bani ko dan taure da zan yi shagali tare da abokaina ba,
30 But when this your son came, who has devoured your living with prostitutes, you killed the fattened calf for him.’
amma da dan nan naka ya zo wanda ya fallasar da dukiyarka a kan karuwai, ka yanka masa kiwataccen marakin nan.
31 “He said to him, ‘Son, you are always with me, and all that is mine is yours.
Sai mahaifin ya ce masa, 'Dana, ai kullum kana tare da ni, duk abin da yake nawa naka ne.
32 But it was appropriate to celebrate and be glad, for this, your brother, was dead, and is alive again. He was lost, and is found.’”
Amma, daidai ne a yi murna da farinciki, don dan'uwan nan naka da ya mutu, amma yanzu yana da rai, da ya bata, amma yanzu an same shi.'”

< Luke 15 >