< John 15 >

1 “I am the true vine, and my Father is the farmer.
“Ni ne kuringar inabi na gaskiya, Ubana kuwa shi ne manomin.
2 Every branch in me that doesn’t bear fruit, he takes away. Every branch that bears fruit, he prunes, that it may bear more fruit.
Yakan sare kowane reshe a cikina da ba ya’ya’ya, amma yakan ƙundume kowane reshe da yake ba da’ya’ya, domin yă ƙara ba da’ya’ya.
3 You are already pruned clean because of the word which I have spoken to you.
Kun riga kun zama masu tsabta saboda maganar da na yi muku.
4 Remain in me, and I in you. As the branch can’t bear fruit by itself unless it remains in the vine, so neither can you, unless you remain in me.
Ku kasance a cikina, ni kuma zan kasance a cikinku. Babu reshen da zai iya yin’ya’ya da kansa, dole yă kasance a jikin kuringar inabin. Haka ku ma, ba za ku iya ba da’ya’ya ba sai kun kasance a cikina.
5 I am the vine. You are the branches. He who remains in me and I in him bears much fruit, for apart from me you can do nothing.
“Ni ne kuringar inabin; ku ne kuma rassan. In mutum ya kasance a cikina ni kuma a cikinsa, zai ba da’ya’ya da yawa; in ba tare da ni ba, ba za ku iya yin kome ba.
6 If a man doesn’t remain in me, he is thrown out as a branch and is withered; and they gather them, throw them into the fire, and they are burned.
Duk wanda bai kasance a cikina ba, yana kamar reshen da aka jefar yă bushe; irin waɗannan rassan ne akan tattara, a jefa cikin wuta a ƙone.
7 If you remain in me, and my words remain in you, you will ask whatever you desire, and it will be done for you.
In kun kasance a cikina kalmomina kuma suka kasance a cikinku, ku roƙi kome da kuke so, za a kuwa ba ku.
8 “In this my Father is glorified, that you bear much fruit; and so you will be my disciples.
Wannan ne yakan kawo ɗaukaka ga Ubana, ku ba da’ya’ya da yawa, kuna kuma nuna kanku ku almajiraina ne.
9 Even as the Father has loved me, I also have loved you. Remain in my love.
“Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma na ƙaunace ku. To, fa, ku kasance cikin ƙaunata.
10 If you keep my commandments, you will remain in my love, even as I have kept my Father’s commandments and remain in his love.
In kuka yi biyayya da umarnaina, za ku kasance a cikin ƙaunata, kamar dai yadda na yi biyayya da umarnan Ubana na kuma kasance a cikin ƙaunarsa.
11 I have spoken these things to you, that my joy may remain in you, and that your joy may be made full.
Na gaya muku wannan domin murnata ta kasance a cikinku, murnanku kuma ta zama cikakkiya.
12 “This is my commandment, that you love one another, even as I have loved you.
Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku.
13 Greater love has no one than this, that someone lay down his life for his friends.
Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa.
14 You are my friends if you do whatever I command you.
Ku abokaina ne, in kun yi abin da na umarta.
15 No longer do I call you servants, for the servant doesn’t know what his lord does. But I have called you friends, for everything that I heard from my Father, I have made known to you.
Ba zan ƙara ce da ku bayi ba, don bawa bai san abin da maigidansa yake yi ba. A maimako in ce da ku abokai, domin na sanar da ku duk abin da na ji daga wurin Ubana.
16 You didn’t choose me, but I chose you and appointed you, that you should go and bear fruit, and that your fruit should remain; that whatever you will ask of the Father in my name, he may give it to you.
Ba ku kuka zaɓe ni ba, a’a, ni ne na zaɓe ku na kuma naɗa ku ku je ku ba da’ya’ya-’ya’yan da za su dawwama. Uba kuwa zai ba ku duk abin da kuka roƙa cikin sunana.
17 “I command these things to you, that you may love one another.
Umarnina ke nan. Ku ƙaunaci juna.
18 If the world hates you, you know that it has hated me before it hated you.
“In duniya ta ƙi ku, ku san cewa ta fara ƙin na ne.
19 If you were of the world, the world would love its own. But because you are not of the world, since I chose you out of the world, therefore the world hates you.
Da ku na duniya ne, da ta ƙaunaci abinta. Kamar yadda yake, ku ba na duniya ba ne, na zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku.
20 Remember the word that I said to you: ‘A servant is not greater than his lord.’ If they persecuted me, they will also persecute you. If they kept my word, they will also keep yours.
Ku tuna da kalmomin da na yi muku cewa, ‘Ba bawan da ya fi maigidansa,’In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun yi biyayya da koyarwata, da za su yi biyayya da taku ma.
21 But they will do all these things to you for my name’s sake, because they don’t know him who sent me.
Za su yi muku haka saboda sunana, gama ba su san Wannan da ya aiko ni ba.
22 If I had not come and spoken to them, they would not have had sin; but now they have no excuse for their sin.
Da a ce ban zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Yanzu kam, ba su da wata hujja a kan zunubinsu.
23 He who hates me, hates my Father also.
Wanda ya ƙi ni ya ƙi ya ƙi Ubana ma.
24 If I hadn’t done among them the works which no one else did, they wouldn’t have had sin. But now they have seen and also hated both me and my Father.
Da a ce ban yi ayyuka a cikinsu waɗanda babu wani da ya taɓa yi ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun ga waɗannan ayyukan banmamaki, duk da haka sun ƙi ni sun kuma ƙi Ubana.
25 But this happened so that the word may be fulfilled which was written in their law, ‘They hated me without a cause.’
Amma wannan ya faru ne domin a cika abin da yake a rubuce cikin Dokarsu cewa, ‘Sun ƙi ni ba dalili.’
26 “When the Counselor has come, whom I will send to you from the Father, the Spirit of truth, who proceeds from the Father, he will testify about me.
“Sa’ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, Ruhun gaskiya wanda yake fitowa daga wurin Uba, zai ba da shaida game da ni.
27 You will also testify, because you have been with me from the beginning.
Ku ma dole ku ba da shaida, domin kun kasance tare da ni tun daga farko.

< John 15 >