< 2 Corinthians 1 >

1 Paul, an apostle of Christ Jesus through the will of God, and Timothy our brother, to the assembly of God which is at Corinth, with all the saints who are in the whole of Achaia:
Bulus, manzon Almasihu Yesu ta wurin nufin Allah, da kuma Timoti dan'uwan mu, zuwa ga Ikilisiyar Allah da ke a Korantus, da kuma dukan 'yan'uwa da ke yankin kasar Akaya.
2 Grace to you and peace from God our Father and the Lord Jesus Christ.
Bari alheri ya kasance tare da ku da kuma salama ta Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Almasihu.
3 Blessed be the God and Father of our Lord Jesus Christ, the Father of mercies and God of all comfort,
Bari yabo ya tabbata ga Allah da kuma Uba na Ubangijinmu Yesu Almasihu. Shine Uba na dukan jiyejiyenkai, da kuma Allah na dukan ta'aziya.
4 who comforts us in all our affliction, that we may be able to comfort those who are in any affliction, through the comfort with which we ourselves are comforted by God.
Allah yana ta'azantar da mu a cikin dukan wahalarmu, domin mu iya ta'azantar da wadanda ke cikin kowace wahala. Muna ta'azantar da wasu da irin ta'aziyar da Allah ke ta'azantar da mu.
5 For as the sufferings of Christ abound to us, even so our comfort also abounds through Christ.
Gama kamar yadda wahalhalun Almasihu suka karu domin mu, haka kuma ta'aziyarmu ta yawaita cikin Almasihu.
6 But if we are afflicted, it is for your comfort and salvation. If we are comforted, it is for your comfort, which produces in you the patient enduring of the same sufferings which we also suffer.
Amma fa idan muna shan wuya, domin ta'aziyarku ne da cetonku. Haka kuma in mun ta'azantu, domin ta'aziyarku ne. Ta'aziyarku tana aiki ne sosai yayinda kuka jure da irin shan wuyar da mu ma muke sha.
7 Our hope for you is steadfast, knowing that, since you are partakers of the sufferings, so you are also of the comfort.
Kuma gabagadinmu game da ku tabbatacce ne. Mun kuwa sani kamar yadda kuke tarayya cikin shan wahalhalun, haka kuma za ku yi tarayya cikin ta'aziyyar.
8 For we don’t desire to have you uninformed, brothers, concerning our affliction which happened to us in Asia: that we were weighed down exceedingly, beyond our power, so much that we despaired even of life.
Gama ba mu so ku rasa sani, 'yan'uwa, game da tsananin da ya same mu a Asiya. An murkushe mu gaba daya har fiye da karfin mu, har ma mun fidda zuciya za mu rayu.
9 Yes, we ourselves have had the sentence of death within ourselves, that we should not trust in ourselves, but in God who raises the dead,
Hakika, mun ji hukuncin mutuwa akan mu. Amma wannan ya faru ne domin kada mu dogara ga kanmu, sai dai ga Allah, wanda ke tada matattu.
10 who delivered us out of so great a death, and does deliver, on whom we have set our hope that he will also still deliver us,
Ya kubutar da mu daga wannan mummunan hatsari na mutuwa, kuma zai sake kubutar da mu. Mun kafa begenmu gare shi cewa zai sake kubutar da mu.
11 you also helping together on our behalf by your supplication; that, for the gift given to us by means of many, thanks may be given by many persons on your behalf.
Zai aikata wannan yayinda kuka taimake mu da addu'ar ku. Sa'an nan da dama za su bada godiya a madadin mu don tagomashin alheri da aka yi mana ta wurin addu'o'in mutane masu yawa.
12 For our boasting is this: the testimony of our conscience that in holiness and sincerity of God, not in fleshly wisdom but in the grace of God, we behaved ourselves in the world, and more abundantly toward you.
Muna kuwa alfahari da haka: wato shaidar lamirinmu. Gama da kyakkyawan nufi da aminci da ke zuwa daga Allah muka tafiyar da rayuwarmu a Duniya. Mun yi wannan ne musamman tare da ku-ba kuwa cikin hikimar Duniya ba, amma ta wurin alherin Allah.
13 For we write no other things to you than what you read or even acknowledge, and I hope you will acknowledge to the end—
Bamu rubuta maku abinda ba za ku iya karantawa ko fahimta ba. Ina fata za ku fahimce mu baki daya,
14 as also you acknowledged us in part—that we are your boasting, even as you also are ours, in the day of our Lord Jesus.
kamar yadda kuka fahimce mu kadan yanzu. Daganan a ranar Ubangijinmu Yesu za mu zama dalilinku na alfahari, kamar yadda za ku zama namu.
15 In this confidence, I was determined to come first to you, that you might have a second benefit,
Saboda gabagadin da nake da shi game da haka, naso in zo gare ku da farko, domin ku amfana da ziyara sau biyu.
16 and by you to pass into Macedonia, and again from Macedonia to come to you, and to be sent forward by you on my journey to Judea.
Ina da shirin ziyaratar ku a kan hanyata ta zuwa Makidoniya. Daga nan kuma ina da yi niyyar in sake ziyartar ku, a tafiya ta daga Makidoniya, domin ku aike ni a hanyata ta zuwa Yahudiya.
17 When I therefore planned this, did I show fickleness? Or the things that I plan, do I plan according to the flesh, that with me there should be the “Yes, yes” and the “No, no?”
Yayinda nake irin wannan tunani, ina shakka ne? Ina shirya abubuwa ne bisa ga magwajin mutum, ta yadda har zan ce “I, i” da “A, a, a, a” a lokaci guda?
18 But as God is faithful, our word toward you was not “Yes and no.”
Amma kamar yadda Allah yake amintacce, ba ma fadin ''I'' da ''A'a'' a lokaci guda.
19 For the Son of God, Jesus Christ, who was preached among you by us—by me, Silvanus, and Timothy—was not “Yes and no,” but in him is “Yes.”
Gama Dan Allah, Yesu Almasihu, wanda Silbanus da Sila, da Ni muka shaida maku, ba “I” da “A, a” ba ne. Maimakon haka, Shi “I” ne a kodayaushe.
20 For however many are the promises of God, in him is the “Yes.” Therefore also through him is the “Amen”, to the glory of God through us.
Gama dukan alkawaran Allah 'I' ne a cikin sa. Haka kuma ta wurin sa muna cewa ''Amin'' zuwa ga daukakar Allah.
21 Now he who establishes us with you in Christ and anointed us is God,
Yanzu dai Allah ne ya tabbatar da mu da ku a cikin Almasihu, ya kuma kebe mu.
22 who also sealed us and gave us the down payment of the Spirit in our hearts.
Ya sa hatiminsa a kan mu ya kuma ba mu Ruhu a zuciyar mu a matsayin tabbacin abinda zai bamu daga baya.
23 But I call God for a witness to my soul, that to spare you, I didn’t come to Corinth.
Maimakon haka, na yi kira ga Allah ya zama shaida domina, cewa dalilin dayasa banzo Korintis ba domin in kare ku ne.
24 We don’t control your faith, but are fellow workers with you for your joy. For you stand firm in faith.
Ba muna kokarin mu sarrafa yadda bangaskiyar ku za ta zama ba ne. Maimakon haka, muna aiki tare da ku ne domin farincikinku, yayinda kuke tsaye cikin bangaskiyarku.

< 2 Corinthians 1 >