< 1 Chronicles 25 >

1 Moreover, David and the captains of the army set apart for the service certain of the sons of Asaph, of Heman, and of Jeduthun, who were to prophesy with harps, with stringed instruments, and with cymbals. The number of those who did the work according to their service was:
Dawuda tare da shugabannin mayaƙa, suka keɓe waɗansu daga’ya’yan Asaf, Heman da Yedutun don hidimar yin annabci, suna amfani da garayu, molaye da ganguna. Ga jerin mutanen da suka yi wannan hidima.
2 of the sons of Asaph: Zaccur, Joseph, Nethaniah, and Asharelah. The sons of Asaph were under the hand of Asaph, who prophesied at the order of the king.
Daga’ya’yan Asaf, Zakkur, Yusuf, Netaniya da Asarela.’Ya’yan Asaf sun kasance a ƙarƙashin kulawar Asaf, wanda ya yi annabci a ƙarƙashin kulawar sarki.
3 Of Jeduthun, the sons of Jeduthun: Gedaliah, Zeri, Jeshaiah, Shimei, Hashabiah, and Mattithiah, six, under the hands of their father Jeduthun, who prophesied in giving thanks and praising Yahweh with the harp.
Game da Yedutun kuwa, daga’ya’yansa maza. Gedaliya, Zeri, Yeshahiya, Shimeyi, Hashabiya da Mattitiya, su shida ne duka, a ƙarƙashin kulawar mahaifinsu Yedutun, wanda ya yi annabci, yana amfani da garaya a yin godiya da yabon Ubangiji.
4 Of Heman, the sons of Heman: Bukkiah, Mattaniah, Uzziel, Shebuel, Jerimoth, Hananiah, Hanani, Eliathah, Giddalti, Romamti-Ezer, Joshbekashah, Mallothi, Hothir, and Mahazioth.
Game da Heman kuwa, daga’ya’yansa maza. Bukkiya, Mattaniya, Uzziyel, Shebuwel, Yerimot; Hananiya, Hanani, Eliyata, Giddalti, Romamti-Ezer, Yoshbekasha, Malloti, Hotir da Mahaziyot.
5 All these were the sons of Heman the king’s seer in the words of God, to lift up the horn. God gave to Heman fourteen sons and three daughters.
Dukan waɗannan’ya’yan Heman ne mai duba na sarki. An ba shi su ta wurin alkawarin Allah don yă ɗaukaka shi. Allah ya ba Heman’ya’ya maza goma sha huɗu da’ya’ya mata uku.
6 All these were under the hands of their father for song in Yahweh’s house, with cymbals, stringed instruments, and harps, for the service of God’s house: Asaph, Jeduthun, and Heman being under the order of the king.
Dukan waɗannan mutane suna a ƙarƙashin kulawar mahaifansu don kaɗe-kaɗe da bushe-bushe a cikin haikalin Ubangiji, da ganguna, molaye da garayu, don hidima a gidan Allah. Asaf, Yedutun da Heman suna ƙarƙashin kulawar sarki.
7 The number of them, with their brothers who were instructed in singing to Yahweh, even all who were skillful, was two hundred eighty-eight.
Da su da danginsu, dukansu su 288 ne kuma horarru da ƙwararru ne a kaɗe-kaɗe da bushe-bushe domin Ubangiji.
8 They cast lots for their offices, all alike, the small as well as the great, the teacher as well as the student.
Baba ko yaro, malami ko ɗalibi, duk suka jefa ƙuri’a saboda ayyukan da za su yi.
9 Now the first lot came out for Asaph to Joseph; the second to Gedaliah, he and his brothers and sons were twelve;
Ƙuri’a ta fari, wadda take don Asaf, ta fāɗo a kan Yusuf,’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta biyu a kan Gedaliya, danginsa da’ya’yansa maza, 12
10 the third to Zaccur, his sons and his brothers, twelve;
ta uku a kan Zakkur,’ya’yansa da danginsa, 12
11 the fourth to Izri, his sons and his brothers, twelve;
ta huɗu a kan Izri,’ya’yansa maza da danginsa, 12
12 the fifth to Nethaniah, his sons and his brothers, twelve;
ta biyar a kan Netaniya,’ya’yansa maza da danginsa, 12
13 the sixth to Bukkiah, his sons and his brothers, twelve;
ta shida a kan Bukkiya,’ya’yansa maza da danginsa, 12
14 the seventh to Jesharelah, his sons and his brothers, twelve;
ta bakwai a kan Yesarela,’ya’yansa maza da danginsa, 12
15 the eighth to Jeshaiah, his sons and his brothers, twelve;
ta takwas a kan Yeshahiya,’ya’yansa maza da danginsa, 12
16 the ninth to Mattaniah, his sons and his brothers, twelve;
ta tara a kan Mattaniya,’ya’yansa maza da danginsa, 12
17 the tenth to Shimei, his sons and his brothers, twelve;
ta goma a kan Shimeyi,’ya’yansa maza da danginsa, 12
18 the eleventh to Azarel, his sons and his brothers, twelve;
ta goma sha ɗaya a kan Azarel,’ya’yansa maza da danginsa, 12
19 the twelfth to Hashabiah, his sons and his brothers, twelve;
ta goma sha biyu a kan Hashabiya,’ya’yansa maza da danginsa, 12
20 for the thirteenth, Shubael, his sons and his brothers, twelve;
ta goma sha uku a kan Shubayel,’ya’yansa maza da danginsa, 12
21 for the fourteenth, Mattithiah, his sons and his brothers, twelve;
ta goma sha huɗu a kan Mattitiya,’ya’yansa maza da danginsa, 12
22 for the fifteenth to Jeremoth, his sons and his brothers, twelve;
ta goma sha biya a kan Yeremot,’ya’yansa maza da danginsa, 12
23 for the sixteenth to Hananiah, his sons and his brothers, twelve;
ta goma sha shida a kan Hananiya, na goma sha biya a kan Yerimot,’ya’yansa maza da danginsa, 12
24 for the seventeenth to Joshbekashah, his sons and his brothers, twelve;
ta goma sha bakwai a kan Yoshbekasha, na goma sha biya a kan Yerimot,’ya’yansa maza da danginsa, 12
25 for the eighteenth to Hanani, his sons and his brothers, twelve;
ta goma sha takwas a kan Hanani, na goma sha biya a kan Yerimot,’ya’yansa maza da danginsa 12
26 for the nineteenth to Mallothi, his sons and his brothers, twelve;
ta goma sha tara a kan Malloti, na goma sha biya a kan Yerimot,’ya’yansa maza da danginsa, 12
27 for the twentieth to Eliathah, his sons and his brothers, twelve;
ta ashirin a kan Eliyata, na goma sha biya a kan Yerimot,’ya’yansa maza da danginsa, 12
28 for the twenty-first to Hothir, his sons and his brothers, twelve;
ta ashirin da ɗaya a kan Hotir, na goma sha biya a kan Yerimot,’ya’yansa maza da danginsa, 12
29 for the twenty-second to Giddalti, his sons and his brothers, twelve;
ta ashirin da biyu a kan Giddalti, na goma sha biya a kan Yerimot,’ya’yansa maza da danginsa, 12
30 for the twenty-third to Mahazioth, his sons and his brothers, twelve;
ta ashirin da uku a kan Mahaziyot, na goma sha biya a kan Yerimot,’ya’yansa maza da danginsa, 12
31 for the twenty-fourth to Romamti-Ezer, his sons and his brothers, twelve.
ta ashirin da huɗu a kan Romamti-Ezer, na goma sha biya a kan Yerimot,’ya’yansa maza da danginsa 12.

< 1 Chronicles 25 >