< Ruth 2 >

1 Now Naomi was related through her husband to a very wealthy man of the family of Elimelech named Boaz.
To, fa, Na’omi tana da dangi a gefen mijinta da iyalin Elimelek, mutum mai martaba, mai suna Bowaz.
2 Ruth the Moabite said to Naomi, ‘Let me now go into the fields and gather leftover grain behind anyone who will allow me.’ ‘Go, my daughter,’ she replied.
Sai Rut mutuniyar Mowab ta ce wa Na’omi, “Bari in tafi gonaki in yi kala raguwar hatsi a bayan duk wanda na sami tagomashi daga gare shi.” Na’omi ta ce mata, “Ki je,’yata.”
3 So she went to glean in the field after the reapers. As it happened, she was in that part of the field which belonged to Boaz, who was of the family of Elimelech.
Saboda haka ta tafi ta fara kala a gonaki a bayan masu girbi. Sai ya zamana, ta sami kanta tana aiki a gonar da take ta Bowaz, wanda yake daga dangin Elimelek.
4 When Boaz came from Bethlehem and said to the reapers, ‘The Lord be with you,’ they answered him, ‘May the Lord bless you.’
Sai ga Bowaz ya iso daga Betlehem ya gai da masu girbi, “Ubangiji yă kasance tare da ku!” Sai suka amsa, “Ubangiji yă albarkace ka!”
5 ‘Whose girl is this?’ Boaz asked his servant who had charge of the reapers.
Sai Bowaz ya tambayi shugaban masu girbinsa, “Wace yarinya ce wannan?”
6 The servant who had charge of the reapers replied, ‘It is the Moabite girl who came back with Naomi from the territory of Moab.
Shugaban ya amsa, “Ita ce mutuniyar Mowab da ta zo daga Mowab tare da Na’omi.
7 She asked to be allowed to glean and gather sheaves after the reapers. So she came and has continued to work until now and she has not rested a moment in the field.’
Ta ce, ‘Ina roƙo a bar ni in bi bayan masu girbin in yi kala.’ Haka ta shiga cikin gonar ta kuwa yi aiki tun da safe har zuwa yanzu, sai ɗan hutun da ta yi kaɗan.”
8 Then Boaz said to Ruth, ‘Listen, my daughter. Do not go to glean in another field nor leave this place, but stay here with my girls.
Saboda haka Bowaz ya ce wa Rut, “’Yata, ki saurare ni. Kada ki tafi ki yi kala a wani gona, kada kuma ki tafi daga nan. Ki tsaya nan tare da’yan matana bayi.
9 Watch where the men are reaping and follow the gleaners. I have told the young men not to trouble you. When you are thirsty, go to the jars and drink of that which the young men have drawn.’
Ki lura da gonar da mutanena suke girbi, ki bi su tare da’yan matana. Na riga na faɗa wa mazan kada su taɓa ke. Kuma duk sa’ad da kika ji ƙishirwa, ki tafi ki ɗebo ruwa daga tulunan da mazan suka cika.”
10 Then she bowed low and said to him, ‘Why are you so kind to me, to take interest in me when I am just a foreigner?’
Jin haka, sai ta rusuna da fuskata har ƙasa ta ce, “Me ya sa na sami irin wannan tagomashi a idanunka da har ka lura da ni, ni da nake baƙuwa?”
11 Boaz replied, ‘I have heard what you have done for your mother-in-law since the death of your husband, and how you left your father and mother and your native land to come to a people that you did not know before.
Bowaz ya amsa, “An faɗa mini duka game da abin kika yi domin surukarki tun mutuwar mijinki, yadda kika bar mahaifinki da mahaifiyarki da kuma ƙasarki kika zo ki yi zama da mutanen da ba ki taɓa sani ba.
12 May the Lord repay you for what you have done, and may you be fully rewarded by the God of Israel, under whose wings you have come to take refuge.’
Bari Ubangiji yă sāka maka saboda abin da ka yi. Bari Ubangiji, Allah na Isra’ila yă sāka maka a yalwace, a ƙarƙashin fikafikan da ka sami mafaka.”
13 Then she said, ‘I trust I may please you, my lord, for you have comforted me and spoken kindly to your servant, although I am not really equal to one of your own servants.’
Ta ce, “Bari in ci gaba da samun tagomashi a idanunka ranka yă daɗe. Ka ta’azantar da ni ka kuma yi wa baranyarka magana mai alheri ko da yake ban kai matsayi ɗaya daga cikin bayinka’yan mata ba.”
14 At mealtime Boaz said to Ruth, ‘Come here and eat some of the food and dip your piece of bread in the vinegar.’ So she sat beside the reapers, and he passed her some roasted grain. She ate until she was satisfied and had some left.
A lokacin cin abinci Bowaz ya ce mata, “Zo nan. Ki ɗebo burodi ki tsoma cikin ruwan inabi.” Da ta zauna tare da masu girbin, sai ya ba ta gasasshe hatsi. Ta ci duk abin da take so har ta bar ragowa.
15 When she rose to glean, Boaz gave this order to his young men: ‘Let her glean even among the sheaves and do not disturb her.
Da ta tashi don tă yi kala, sai Bowaz ya yi umarni wa samarinsa cewa, “Ko ta tara daga cikin dammuna, kada ku wulaƙanta ta.
16 Also pull out some for her from the bundles and leave for her to glean, and do not find fault with her.’
Ku kuma riƙa zarar mata waɗansu daga dammunan don ta ɗauka, kada ku kwaɓe ta.”
17 So she gleaned in the field until evening, then beat out what she had gleaned. It was about a bushel of barley.
Saboda haka Rut ta yi kala a gonar har yamma. Sa’an nan ta sussuka hatsin sha’ir da ta kalata ta sami kamar efa.
18 Then she took it up and went into the town and showed her mother-in-law what she had gleaned. She also brought out and gave her that which she had left from her meal after she had had enough.
Ta ɗauka ta koma gari sai surukarta ta ga yawan abin da ta kalato. Rut kuma ta fitar da ragowar abin da ta ci bayan ta ƙoshi ta ba ta.
19 ‘Where did you glean today, and where did you work?’ asked her mother-in-law. ‘A blessing on him who took notice of you!’ So she told her mother-in-law where she had worked. ‘The name of the man with whom I worked today,’ she said, ‘is Boaz.’
Surukarta ta tambaye ta, “Ina kika yi kala a yau? Ina kika yi aiki? Albarka ta tabbata ga mutumin nan ta ya lura da ke!” Sai Rut ta faɗa wa surukarta game da wurin wanda ta yi ta aiki. Ta ce, “Sunan mutumin da na yi aiki da shi a yau Bowaz ne.”
20 Naomi said to her daughter-in-law, ‘May the blessing of the Lord rest on this man who has not ceased to show his loving-kindness to the living and to the dead. The man,’ she added, ‘is a near relation of ours.’
Sai Na’omi ta ce wa surukarta, “Ubangiji yă yi masa albarka! Bai daina nuna alheri ga masu rai da matattu ba.” Ta ƙara da cewa, “Wannan mutum danginmu ne na kusa; shi ɗaya daga cikin danginmu mai fansa.”
21 ‘He told me,’ Ruth said, ‘that I must keep near his young men until they have completed all his harvest.’
Sa’an nan Rut mutuniyar Mowab ta ce, “Ya ma ce mini, ‘Ki riƙa bin ma’aikatana sai sun ƙare yin girbin dukan hatsina.’”
22 Naomi said to Ruth, ‘It is best, my daughter, that you should go out with his girls because you might not be as safe in another field.’
Na’omi ta ce wa Rut surukarta, “Zai fi miki kyau,’yata ki riƙa tafiya da’yan matansa, domin a gonar wani dabam mai yiwuwa a yi miki lahani.”
23 So she gleaned with the girls of Boaz until the end of the barley and wheat harvest; but she lived with her mother-in-law.
Saboda haka Rut ta tsaya kusa da bayi mata na Bowaz don tă yi kala sai da girbin sha’ir da na alkama suka ƙare. Ta kuwa zauna tare da surukarta.

< Ruth 2 >