< Leviticus 4 >

1 The Lord told Moses,
Ubangiji ya ce wa Musa,
2 “Tell the Israelites that these are the rules to handle cases of those who sin unintentionally against any of the Lord's commandments and do what is not permitted.
“Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Sa’ad da wani ya yi zunubi ba da gangan ba, har ya karya ɗaya daga cikin dokokin Ubangiji,
3 If it is the high priest who sins and brings guilt on everyone, he must present to the Lord a young bull without defects as a sin offering for his sin.
“‘In shafaffen firist ya yi zunubi, ya jawo wa jama’a laifi, dole yă kawo wa Ubangiji ɗan bijimi marar lahani a matsayin hadaya don zunubi saboda zunubin da ya yi.
4 He must take the bull to the entrance of the Tent of Meeting before the Lord, put his hand on its head and kill it before the Lord.
Zai kawo bijimin a ƙofar Tentin Sujada a gaban Ubangiji. Zai ɗibiya hannunsa a kan bijimin, yă kuma yanka shi a gaban Ubangiji.
5 Then the high priest shall take some of the bull's blood into the Tent of Meeting.
Sa’an nan shafaffen firist zai ɗiba jinin bijimin yă kai cikin Tentin Sujada.
6 The high priest shall dip his finger in the blood and sprinkle some of it seven times before the Lord in front of the veil of the sanctuary.
Yă tsoma yatsarsa a cikin jinin, yă kuma yafa sau bakwai a gaban Ubangiji, a gaban labulen wuri mai tsarki.
7 The priest shall put some of the blood on the horns of the altar of aromatic incense that stands before the Lord in the Tent of Meeting. The rest of the bull's blood he is to pour out at the bottom of the altar of burnt offering at the entrance to the Tent of Meeting.
Sa’an nan firist ɗin zai zuba jinin a ƙahonin bagaden turare masu ƙanshi da suke a gaban Ubangiji a Tentin Sujada. Sauran jinin bijimin zai zuba a gindin bagaden hadaya ta ƙonawa a ƙofar zuwa Tentin Sujada.
8 Then he shall remove all the fat from the bull of the sin offering: all the fat that covers the insides,
Zai cire dukan kitsen daga bijimin hadaya don zunubi, kitsen da ya rufe kayan cikin, ko kuwa da suka shafe su,
9 both kidneys with the fat on them by the loins, and the best part of the liver, which he is to remove together with the kidneys
da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta, waɗanda zai cire tare da ƙodoji.
10 in the same way as the fat is removed from the bull of the peace offering. Then the priest shall then burn this on the altar of burnt offering.
Zai cire su daidai kamar yadda akan cire na bijimin hadaya ta salama. Sai firist ɗin yă ƙone su a kan bagaden ƙona hadaya.
11 But the skin of the bull, all its flesh, head, legs, insides and waste—
Amma fatar ɗan bijimin, da namansa, da kansa, da ƙafafunsa, da kayan cikinsa, da hanjinsa,
12 all the rest of it—he has to take outside the camp to a place that is ceremonially clean, where the ashes are dumped, and he must burn it on a wood fire there on the ash heap.
wato, dukan sauran bijimi, dole yă ɗauke su zuwa waje da sansani zuwa wani wuri mai tsabta inda ake zub da toka, yă ƙone shi a itacen da yake cin wuta a tarin toka.
13 If the whole Israelite community goes astray unintentionally, and even though they are unaware of doing what is not permitted by any of the Lord's commandments, they are all still guilty.
“‘In dukan jama’ar Isra’ilawa suka yi zunubi ba da gangan ba, har suka aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, ko da yake jama’ar ba su san batun ba, duk da haka sun yi laifi.
14 When they realize their sin, then they must bring a young bull as a sin offering and present it before the Tent of Meeting.
Sa’ad da suka gane da zunubin da suka aikata, dole taron su kawo ɗan bijimi a matsayin hadaya don zunubi, su kawo shi a gaban Tentin Sujada.
15 The elders of Israel are to put their hands on its head and kill it before the Lord.
Dattawan jama’a za su ɗibiya hannuwansu a kan bijimin a gaban Ubangiji, sai a yanka bijimin a gaban Ubangiji.
16 Then the high priest shall take some of the bull's blood into the Tent of Meeting.
Sa’an nan shafaffen firist zai ɗibi jinin bijimi zuwa cikin Tentin Sujada.
17 He shall dip his finger in the blood and sprinkle it seven times before the Lord in front of the veil.
Zai tsoma yatsarsa cikin jini yă kuma yayyafa shi a gaban Ubangiji sau bakwai a gaban labule.
18 He shall put some of the blood on the horns of the altar that stands before the Lord in the Tent of Meeting. Then he is to pour out the rest of the bull's blood at the bottom of the altar of burnt offering at the entrance to the Tent of Meeting.
Zai zuba jinin a ƙahonin bagaden da suke gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada. Zai zuba sauran jinin a gindin bagaden hadaya ta ƙonawa a ƙofar zuwa Tentin Sujada.
19 Then he shall remove all the fat from the bull and burn it on the altar.
Zai cire dukan kitsen daga gare shi yă ƙone a kan bagade,
20 He shall offer this bull in the same way he did for the sin offering. This is how the priest will make them right, and they will be forgiven.
yă kuma yi da wannan bijimi kamar yadda ya yi da bijimi na hadaya don zunubi. Ta haka firist zai yi kafara dominsu, za a kuwa gafarta musu.
21 Then he shall take the bull outside the camp and burn it, just as he burned the bull previously mentioned. It is the sin offering for the whole community.
Sa’an nan zai ɗauki bijimin waje da sansani yă ƙone shi kamar yadda ya ƙone bijimi na fari. Wannan ita ce hadaya don zunubi domin jama’a.
22 If a leader sins unintentionally and does what is not permitted by any of the commandments of the Lord his God, he is guilty.
“‘Sa’ad da shugaba ya yi zunubi ba da gangan ba, har ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji Allahnsa ya umarta, to, ya yi laifi.
23 When he realizes his sin, he must bring a male goat without defects as his offering.
Sa’ad da aka sanar da shi game da zunubin da ya yi, dole yă kawo bunsuru marar lahani a matsayin hadayarsa.
24 He must put his hand on the head of the goat and kill it at the place where the burnt offering is killed before the Lord. It is a sin offering.
Zai ɗibiya hannunsa a kan bunsurun yă kuma yanka shi a inda ake yankan hadayar ƙonawa a gaban Ubangiji. Hadaya ce ta zunubi.
25 Then the priest is to take some of the blood of the sin offering with his finger and put it on the horns of the altar of burnt offering, and pour out the rest of the blood at the bottom of the altar.
Sa’an nan firist zai ɗibi jinin hadaya don zunubi da yatsarsa yă sa a ƙahonin bagaden hadayar ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a gindin bagade.
26 He shall burn all its fat on the altar like the fat of the peace offerings. In this way the priest will make the man's sin right, and he will be forgiven.
Zai ƙone dukan kitse a kan bagade kamar yadda ya ƙone kitsen hadaya ta salama. Ta haka firist zai yi kafara saboda zunubin mutumin, za a kuwa gafarta masa.
27 If any other Israelite sins unintentionally and does what is not permitted by any of the commandments of the Lord his God, he is guilty.
“‘In wani memba a cikin jama’a ya yi zunubi ba da gangan ba, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, to, ya yi laifi.
28 When he realizes his sin, he must bring a female goat without defects as his offering for that sin.
Sa’ad da aka sanar da shi game da zunubin da ya yi, dole yă kawo akuya marar lahani a matsayin hadayarsa domin zunubin da ya yi.
29 He must put his hand on the head of the sin offering and kill it at the place at the place of the burnt offering.
Zai ɗibiya hannunsa a kan hadaya don zunubin yă kuma yanka ta a inda ake hadaya ta ƙonawa.
30 Then the priest is to take some of its blood with his finger and put it on the horns of the altar of burnt offering, and pour out the rest of the blood at the bottom of the altar.
Sa’an nan firist zai ɗibi jinin da yatsarsa yă zuba a ƙahoni a bagaden hadaya ta ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a ƙasan bagade.
31 He shall remove all its fat like the fat of the peace offerings and burn it on the altar and it will be to be accepted by the Lord. In this way the priest will make the man's sin right, and he will be forgiven.
Za a ɗebe kitsenta duka kamar yadda akan ɗebe kitsen hadaya ta salama. Firist zai ƙona shi a kan bagaden don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Ta haka firist zai yi kafara dominsa, za a kuwa gafarta masa.
32 If he brings a lamb as a sin offering, he is to bring a female without defects.
“‘Idan kuwa daga cikin’yan tumaki zai ba da hadayarsa, sai ya kawo’yar tunkiya marar lahani.
33 He must put his hand on the head of the sin offering and kill it as a sin offering at the place at the place where the burnt offering is killed.
Zai ɗibiya hannunsa a kanta yă kuma yanka ta hadaya don zunubi a inda ake yankan hadayar ƙonawa.
34 Then the priest is to take some of its blood with his finger and put it on the horns of the altar of burnt offering, and pour out the rest of the blood at the bottom of the altar.
Sa’an nan firist zai ɗibi jinin hadaya don zunubin da yatsarsa yă zuba a ƙahonin bagaden hadayar ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a gindin bagade.
35 He shall remove all its fat like the fat of the lamb is removed from the peace offerings and burn it on the altar and it will be to be accepted by the Lord. In this way the priest will make the man's sin right, and he will be forgiven.
Zai kuma ɗebe kitsenta duka kamar yadda a kan ɗebe na ragon hadaya ta salama. Firist zai ƙone shi a bisa bagaden a bisa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ta haka firist ɗin zai yi kafara dominsa saboda zunubin da ya yi, za a kuwa gafarta masa.

< Leviticus 4 >