< Jeremiah 30 >

1 This is the message that came to Jeremiah from the Lord:
Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga Ubangiji.
2 This is what the Lord, the God of Israel, says: Write down in a book everything I've told you.
“Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Ka rubuta a cikin littafi dukan maganganun da na yi maka.
3 Look, the time is coming, declares the Lord, when I will bring back my people Israel and Judah from captivity, declares the Lord. I will bring them back to the country I gave to their forefathers, and they will own it again.
Kwanaki suna zuwa,’ in ji Ubangiji, ‘sa’ad da zan komo da mutanena Isra’ila da Yahuda daga bauta in kuma maido da su ga ƙasar da na ba wa kakanninsu mallaka,’ in ji Ubangiji.”
4 This what the Lord said about Israel and Judah.
Ga kalmomin Ubangiji da ya yi game da Isra’ila da Yahuda,
5 This is what the Lord says: Hear the cries of panic, cries of fear, not peace.
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, “‘Ana jin kukan tsoro, razana, ba salama ba.
6 Think about it! Can men give birth? No. So why do I see every man holding his stomach with his hands like a woman in labor. Why is every face white as a sheet?
Ku tambaya ku ji. Namiji zai iya haifi’ya’ya? To, me ya sa kuke ganin kowane mai ƙarfi da hannuwansa a kwankwaso kamar mace mai naƙuda, kowace fuska ta koma fari?
7 What a terrible day it will be—a day like never before! This is the time of trouble for Jacob's descendants, but they will be rescued from it.
Kaito, gama wannan rana za tă zama mai girma! Babu kamar ta. Zai zama lokacin wahala wa Yaƙub, amma za a cece shi daga cikinta.
8 On that day, declares the Lord Almighty, I will break the yoke from their necks and tear off their chains. Foreigners won't make them slaves anymore.
“‘A wannan rana,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki, ‘Zan karya karkiya daga wuyansu zan kuma cire musu kangi; baƙi ba za su ƙara bautar da su ba.
9 They will serve the Lord their God, and their king, David's descendant whom I will give them.
A maimakon haka, za su bauta wa Ubangiji Allahnsu Dawuda sarkinsu kuwa, wanda na tayar musu.
10 As far as you're concerned, my servant Jacob, don't be afraid, declares the Lord, Israel, don't be discouraged. I promise to save you from your distant places of exile, your descendants from the countries where they're being held captive. The descendants of Jacob will go home to a quiet and comfortable life, free from any threats.
“‘Saboda haka kada ka ji tsoro, ya Yaƙub bawana; kada ka karai, ya Isra’ila,’ in ji Ubangiji. ‘Tabbatacce zan cece ka daga wuri mai nesa, zuriyarka daga ƙasar zaman bautansu. Yaƙub zai sami salama da zaman lafiya, kuma ba wanda zai sa ya ji tsoro.
11 I am with you and I will save you, declares the Lord. Even though I'm going to completely destroy all the nations where I scattered you, I won't completely destroy you. However, I will discipline you as you deserve, and you can be sure I won't leave you unpunished.
Ina tare da kai zan kuma cece ka,’ in ji Ubangiji. ‘Ko da yake na hallakar da dukan al’umma gaba ɗaya a inda na warwatsa ku, ba zan hallaka ku gaba ɗaya ba. Zan hore ku amma da adalci kaɗai; ba zan ƙyale ku ku tafi gaba ɗaya ba hukunci ba.’
12 This is what the Lord says: You have a wound that cannot be healed, you have a terrible injury.
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, “‘Mikinku marar warkewa ne, raunin da kuka ji ya sha ƙarfin warkarwa.
13 There's no one to take care of your case, no cure for your sores, no healing for you.
Babu wanda zai yi roƙo saboda damuwarku, ba magani domin mikinku babu warkarwa dominku.
14 All your lovers have forgotten about you; they don't bother looking for you anymore, because I have beaten you as if I were your enemy, the discipline of a cruel person, because of how wicked you are, because of your many sins.
Dukan abokanku sun manta da ku; ba su ƙara kulawa da ku. Na buge ku kamar yadda abokin gāba zai yi na kuma hukunta ku yadda mai mugunta zai yi, domin laifinku da girma yake zunubanku kuma da yawa suke.
15 Why are you crying over your wound? You pain can't be cured. I did this to you because of how wicked you are, because of your many sins.
Me ya sa kuke kuka a kan mikinku, wahalarku da ba ta da magani? Domin laifinku da girma yake da kuma zunubanku masu yawa na yi muku waɗannan abubuwa.
16 Even so, everyone who destroys you will be destroyed. All your enemies, every last one, will be sent into exile. Those who plundered you will be plundered, and all who robbed you will be robbed.
“‘Amma duk wanda ya cinye ku za a cinye shi; dukan abokan gābanku za su tafi zaman bauta. Waɗanda suka washe ku su ma za a washe su; dukan waɗanda suka mai da ku ganima su ma zan mai da su ganima.
17 But I will give you back your health and heal your wounds, declares the Lord, because people say you've been abandoned and that no one cares about you, Zion.
Amma zan mayar muku da lafiya in kuma warkar da mikinku,’ in ji Ubangiji, ‘domin ana ce da ku yasassu, Sihiyona wadda ba wanda ya kula da ita.’
18 This is what the Lord says: I will bring Jacob's descendants back to their homes and have mercy on their families. The city will be rebuilt on top of its ruins, and the palace once again stand where it should.
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, “‘Zan mayar da wadatar tentin Yaƙub in kuma ji tausayin wuraren zamansa; za a sāke gina birnin a kufansa, fadar kuwa za tă tsaya a wurin da ya dace da ita.
19 People will be singing songs of thanks, the sounds of celebration. I will increase their number—they will not become less. I will honor them—they will not be treated as insignificant.
Daga gare su waƙoƙi za su fito na godiya da kuma sowa ta farin ciki. Zan riɓaɓɓanya su, ba za su kuwa ragu ba; zan kawo musu ɗaukaka, ba kuwa za a ƙasƙanta su ba.
20 Their children will be looked after like they used to be. I will make their nation strong again, and punish anyone who attacks them.
’Ya’yansu za su kasance kamar a kwanakin dā jama’arsu kuma za su kahu a gabana; zan hukunta duk wanda ya zalunce su.
21 Their leader will be from their own country, their ruler will be chosen from among them. I will invite him to come close to me, and he will do so, for would anyone dare to approach me without being asked? declares the Lord.
Shugabansu zai zama ɗaya daga cikinsu; mai mulkinsu zai taso daga cikinsu. Zan kawo shi kusa zai kuma zo kusa da ni, gama wane ne zai miƙa kansa don yă yi kusa da ni?’ In ji Ubangiji.
22 You will be my people, and I will be your God.
‘Saboda haka za ku zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnku.’”
23 Watch out! The Lord has sent out a furious storm, a tornado swirling around the heads of the wicked.
Ga shi, hadarin Ubangiji zai fasu cikin hasala, iskar guguwa mai hurawa a kan kawunan mugaye.
24 The Lord's anger won't fade until he's finished doing everything he wants. Only then will you really understand.
Fushi mai zafi na Ubangiji ba zai kawu ba sai ya cika manufofin zuciyarsa gaba ɗaya. A kwanaki masu zuwa za ku gane wannan.

< Jeremiah 30 >