< 2 Samuel 3 >

1 There was a long war between those on the side of Saul and those on the side of David. David's side grew stronger, while Saul's side grew weaker.
Aka daɗe ana yaƙi tsakanin gidan Shawulu da gidan Dawuda. Dawuda kuwa ya yi ta ƙara ƙarfi, yayinda gidan Shawulu ya yi ta raguwa a ƙarfi.
2 David's sons born at Hebron were: Amnon (firstborn), by Ahinoam from Jezreel;
An haifa wa Dawuda’ya’ya maza a Hebron. Ɗansa na fari shi ne Amnon, ɗan Ahinowam mutuniyar Yezireyel;
3 Chileab (second), by Abigail, Nabal's widow from Carmel; Absalom (third), by Maacah, daughter of King Talmai of Geshur:
na biyu shi ne Kileyab, ɗan Abigiyel gwauruwar Nabal mutumin Karmel; na uku shi ne Absalom, ɗan Ma’aka’yar Talmai sarkin Geshur;
4 Adonijah (fourth), by Haggith; Shephatiah (fifth), by Abital;
na huɗu shi ne Adoniya, ɗan Haggit; na biyar shi ne Shefatiya, ɗan Abital;
5 Ithream (sixth), by David's wife Eglah. These were the sons born to David at Hebron.
na shida kuma shi ne Itireyam, ɗan Egla matar Dawuda. An haifi waɗannan wa Dawuda a Hebron.
6 Abner had been strengthening his position among the supporters of Saul's dynasty during the war between those on the side of Saul and those on the side of David.
Sa’ad da ake yaƙi tsakanin gidan Shawulu da gidan Dawuda, sai Abner ya yi ta ƙarfafa matsayinsa a gidan Shawulu.
7 Saul had a concubine named Rizpah, daughter of Aiah. One day Ishbosheth accused Abner, saying “Why have you been sleeping with my father's concubine?”
To, Shawulu yana da ƙwarƙwarar da ake kira Rizfa,’yar Aiya. Sai Ish-Boshet ya ce wa Abner, “Don me kake kwana da ƙwarƙwarar mahaifina?”
8 Abner got extremely angry at Ishbosheth accusation. “Am I a dog's head siding with Judah?” he replied. “Right up to the present day I have been loyal to your dynasty—to your father Saul, and to his brothers and friends. I haven't betrayed you to David. But now you dare to accuse me of sinning with this woman!
Abner ya husata saboda abin da Ish-Boshet ya ce, sai ya ce, “Kana tsammani ni mai cin amana ne? Kana zato ni mai goyon bayan Yahuda ne? Tun farko na nuna aminci ga gidan babanka Shawulu, da’yan’uwansa, da abokansa! Ban kuwa ba da kai a hannun Dawuda ba. Ga shi yanzu a kan mace za ka ga laifina?
9 So now may God punish me severely if I don't help David achieve what the Lord has promised him.
Allah yă yi wa Abner hukunci mai tsanani, in ban goyi bayan Dawuda ya sami abin da Ubangiji ya yi masa alkawari da rantsuwa ba.
10 I will hand over the kingdom from Saul's dynasty, and help set up David's rule over Israel and Judah, from Dan to Beersheba.”
Zan kuma mayar wa Dawuda sarautar gidan Shawulu, in kafa kursiyin Dawuda a kan Isra’ila, da kan Yahuda tun daga Dan har zuwa Beyersheba.”
11 Ishbosheth didn't dare to say anything else to Abner because he was frightened of him.
Ish-Boshet bai ƙara yin karambanin ce wa Abner kome ba, gama yana tsoronsa.
12 Then Abner sent messengers to speak for him to David, saying, “Who does the country belong to anyway? Make an agreement with me, and you can be sure I'll be on your side to have all of Israel follow you.”
Sai Abner ya aiki manzanni a madadinsa wurin Dawuda su ce masa, “Ƙasar ta wane ne? Ka yi yarjejjeniya da ni, zan kuwa taimake ka, in juye dukan Isra’ila zuwa ɓangarenka.”
13 “Fine,” David replied, “I'll make an agreement with you. But I have one condition: I won't see you unless you bring Saul's daughter Michal when you come.”
Dawuda ya ce, “Da kyau, zan yi yarjejjeniya da kai, amma fa ina bukata abu guda daga gare ka, kada ka zo gabana in ba tare da matata Mikal,’yar Shawulu ba.”
14 Then David sent messengers tell Ishbosheth, son of Saul, “Give me back my wife Michal—I paid a dowry for her of one hundred Philistine foreskins.”
Sai Dawuda ya aiki manzanni zuwa wurin Ish-Boshet ɗan Shawulu cewa, “Ka ba ni matata Mikal wadda na biya sadakinta da loɓa ɗari na Filistiyawa.”
15 Ishbosheth sent for her and took her away from her husband Paltiel, son of Laish.
Sai Ish-Boshet ya ba da umarni, aka kuwa ɗauke ta daga gidan mijinta Faltiyel ɗan Layish.
16 Her husband followed her to the town of Bahurim, crying as he went. Then Abner ordered him, “Go back home!” So he went home.
Amma mijin ya raka ta, yana tafe yana kuka, ya bi ta har Bahurim. Sai Abner ya ce masa, “Koma gida!” Sai ya koma.
17 Abner spoke with the elders of Israel and said, “For a while now you have wanted to have David as your king.
Abner ya tattauna da dattawan Isra’ila ya ce, “An daɗe kuna nema ku naɗa Dawuda sarkinku.
18 Now is the time to do it, because the Lord promised David, ‘Through my servant David I am going to save my people Israel from the Philistines and all their enemies.’”
To, yanzu sai ku yi haka! Gama Ubangiji ya yi wa Dawuda alkawari ya ce, ‘Ta wurin bawana Dawuda zan ceci mutanena Isra’ila daga hannun Filistiyawa, da kuma hannun dukan abokan gābansu.’”
19 Abner also talked to the people of Benjamin, and went to Hebron to let David know everything that the Israelites and the whole tribe of Benjamin had decided to do.
Abner kuma ya yi magana da mutane Benyamin da kansa. Sa’an nan ya tafi Hebron yă gaya wa Dawuda ko mene ne Isra’ila da kuma dukan gidan Benyamin suke so su yi.
20 Abner came with twenty of his men to see David at Hebron, and David prepared a feast for them.
Sa’ad da Abner wanda yake tare da mutane ashirin suka zo wurin Dawuda a Hebron, Dawuda ya shirya masa liyafa tare da mutanensa.
21 Abner told David, “Let me go immediately and summon all of Israel to come together for my lord the king, so they may make an agreement with you, and that you may rule over all you would wish.” Then David sent Abner safely on his way.
Sai Abner ya ce wa Dawuda, “Bari in tafi nan da nan in tattara dukan Isra’ila wa ranka yă daɗe, sarki, saboda su yi alkawari da kai, ka kuma ka yi mulki bisa dukansu yadda ranka yake so.” Saboda haka Dawuda ya sallami Abner, ya kuwa tafi lafiya.
22 Soon after Joab and David's men came back from a raid, bringing with them a large amount of plunder. However, Abner wasn't there with David in Hebron because David had already sent him safely on his way in peace.
Ba a jima ba sai mutanen Dawuda da Yowab suka dawo daga hari. Suka kawo ganima da yawa tare da su. Abner kuwa ya riga ya bar Dawuda a Hebron, domin Dawuda ya sallame shi, shi kuma ya tafi lafiya.
23 When Joab and all the army that was with him arrived, he was told, “Abner, son of Ner, came to see the king, who sent him safely on his way.”
Sa’ad da Yowab da dukan sojoji suka dawo, aka gaya masa cewa Abner ɗan Ner ya zo wurin sarki, sarki kuwa ya sallame shi, ya kuma tafi lafiya.
24 Joab went to the king and asked, “What do you think you're doing? Here's Abner, who came to see you. Why on earth did you send him on his way? Now he's got clean away!
Sai Yowab ya je wurin sarki ya ce, “Me ke nan ka yi? Abner ya zo wurinka. Don me ka ƙyale shi yă tafi? Ga shi kuwa ya tafi!
25 You do see that Abner, son of Ner, came here to trick you, to spy on the movements of your army, and to find out everything you're doing!”
Ka san Abner ɗan Ner ya zo ne yă ruɗe ka, yă ga fitarka da shigarka, yă kuma binciki kome da kake yi.”
26 When Joab left David, he sent messengers after Abner. They met up with him at the well of Sirah and brought him back, but David didn't know anything about it.
Yowab ya tashi daga gaban Dawuda ya tafi ya aika manzanni su bi Abner. Suka same shi a rijiyar Sira suka komo da shi, Dawuda kuwa bai sani ba.
27 When Abner arrived back in Hebron, Joab took him aside into the town gatehouse as if he was going to talk with him in private. But Joab stabbed him in the belly, killing him in revenge for killing Joab's brother Asahel.
To, da Abner ya komo Hebron, Yowab ya ratse da shi zuwa hanyar shigar gari kamar zai gana da shi a kaɗaice. Amma a can ya soki Abner a ciki, ya kashe shi don yă rama mutuwar ɗan’uwansa Asahel.
28 When David heard about this later he said, “I and my kingdom are totally innocent before the Lord regarding the death of Abner, son of Ner!
Daga baya, Dawuda ya ji labarin sai ya ce, “Ni da masarautata har abada ba mu da laifi a gaban Ubangiji game da jinin Abner ɗan Ner.
29 May the guilt for his death fall on Joab and his family! May Joab's descendants always have someone who has running sores or leprosy or is crippled or who is killed by the sword or who is starving.”
Alhakin jininsa yă kasance a kan Yowab da kuma a kan dukan iyalin mahaifinsa! Kada gidan Yowab yă rasa mai ɗiga, ko kuturu, ko mai jingina ga sanda, ko wanda aka kashe da takobi, ko kuma wanda ba shi da abinci.”
30 (This is why Joab and Abishai his brother killed Abner, because he had killed their brother Asahel during the battle at Gibeon.)
(Yowab da ɗan’uwansa Abishai suka kashe Abner don yă kashe ɗan’uwansu Asahel a yaƙin Gibeyon.)
31 Then David ordered Joab and everyone who was there, “Tear your clothes, put on sackcloth, and mourn for Abner.” King David himself followed the body as it was carried to the grave.
Sa’an nan Dawuda ya ce wa Yowab da dukan mutanen da suke tare da shi, “Ku yayyage rigunarku, ku sa tsummoki, ku yi tafiya kuna kuka a gaban Abner.” Sarki Dawuda kansa ya bi masu ɗauke da gawar daga baya.
32 They buried Abner in Hebron, and the king cried loudly at the grave, along with all the people.
Suka binne Abner a Hebron, sarki kuwa ya ɗaga murya ya yi kuka a kabarin Abner.
33 The king sang this lament for Abner: “Did Abner deserve to die like a criminal?
Sarki ya kuma yi wannan waƙar makoki domin Abner ya ce, “Daidai ne Abner yă mutu, kamar yadda marasa bin doka suke mutuwa?
34 Your hands were not tied together, your feet were not in shackles. But just like a murderer's victim, you too were killed.” All the people cried for him even more.
Hannuwanka ba a daure suke ba, ƙafafunka ba a tabaibaye suke ba. Ka mutu kamar waɗanda suke mutuwa a hannun mugaye.” Sai dukan mutane suka sāke fashe da kuka saboda shi.
35 Then people came to David and tried to persuade him to have something to eat during the day. But David swore an oath, saying, “May God punish me severely if I eat bread or anything else before sunset!”
Sa’an nan duk suka zo suka roƙi Dawuda yă ci wani abu tun rana ba tă fāɗi ba; amma Dawuda ya rantse ya ce, “Bari Allah yă hukunta ni, in na ɗanɗana abinci ko wani abu kafin rana ta fāɗi!”
36 Everyone saw this and thought it was the right thing to do, in the same way that they thought everything the king did was the right thing to do.
Dukan mutane suka lura suka kuma ji daɗi ƙwarai, tabbatacce kome da sarki ya yi, ya gamshe su.
37 That day everyone in Judah and throughout Israel realized that David had not ordered Abner's murder.
Saboda haka a ranar dukan mutane da dukan Isra’ila suka gane sarki ba shi da hannu a kisan Abner ɗan Ner.
38 Then the king said to his officers, “Don't you recognize that a commander and a truly great man has fallen in Israel today?
Sa’an nan sarki ya ce wa mutanensa, “Ba ku gane cewa ɗan sarki kuma babban mutum ya mutu a ƙasar Isra’ila a yau ba?
39 I am weak right now, even though I'm anointed as king and these men, the sons of Zeruiah, are too powerful for me. But may the Lord repay the evil man according to the evil he has done.”
A yau, ko da yake ni naɗaɗɗen sarki ne, duk da haka na raunana, kuma waɗannan’ya’yan Zeruhiya sun fi ƙarfina. Ubangiji yă sāka wa mai aikata mugunta da muguntar da ya aikata!”

< 2 Samuel 3 >