< 马太福音 12 >

1 那时,耶稣在安息日从麦地经过。他的门徒饿了,就掐起麦穗来吃。
A lokacin nan Yesu ya bi ta gonakin hatsi a ranar Asabbaci. Almajiransa kuwa suna jin yunwa, sai suka fara kakkarya kan hatsi suna ci.
2 法利赛人看见,就对耶稣说:“看哪,你的门徒做安息日不可做的事了!”
Sa’ad da Farisiyawa suka ga wannan, sai suka ce masa, “Duba! Almajiranka suna yin abin da doka ta hana a yi a ranar Asabbaci.”
3 耶稣对他们说:“经上记着大卫和跟从他的人饥饿之时所做的事,你们没有念过吗?
Sai ya amsa ya ce, “Ba ku karanta abin da Dawuda ya yi ba ne sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa?
4 他怎么进了 神的殿,吃了陈设饼,这饼不是他和跟从他的人可以吃得,惟独祭司才可以吃。
Ya shiga gidan Allah, da shi da abokan tafiyarsa suka ci keɓaɓɓen burodin, wanda doka ta hana su yi, sai firistoci kaɗai.
5 再者,律法上所记的,当安息日,祭司在殿里犯了安息日还是没有罪,你们没有念过吗?
Ko kuwa ba ku karanta a Doka cewa a ranar Asabbaci firistoci sukan karya dokar Asabbaci duk da haka ba da yin wani laifi ba?
6 但我告诉你们,在这里有一人比殿更大。
Ina faɗa muku cewa waniwanda ya fi haikali yana a nan.
7 ‘我喜爱怜恤,不喜爱祭祀。’你们若明白这话的意思,就不将无罪的当作有罪的了。
Da a ce kun san abin da waɗannan kalmomi suke nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba,’da ba ku zargi marar laifi ba.
8 因为人子是安息日的主。”
Gama Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabbaci.”
9 耶稣离开那地方,进了一个会堂。
Da ya ci gaba daga wurin, sai ya shiga majami’arsu,
10 那里有一个人枯干了一只手。有人问耶稣说:“安息日治病可以不可以?”意思是要控告他。
a nan kuwa akwai wani mutum mai shanyayyen hannu. Don neman dalili su zargi Yesu, sai suka tambaye shi suka ce, “Ya dace a warkar a ranar Asabbaci?”
11 耶稣说:“你们中间谁有一只羊,当安息日掉在坑里,不把它抓住、拉上来呢?
Ya ce musu, “In waninku yana da tunkiya, ta kuma fāɗa a rami ran Asabbaci, ba zai cire ta daga ramin ba?
12 人比羊何等贵重呢!所以,在安息日做善事是可以的。”
Sau nawa mutum ya fi tunkiya daraja! Saboda haka ya dace a aikata alheri ran Asabbaci.”
13 于是对那人说:“伸出手来!”他把手一伸,手就复了原,和那只手一样。
Sa’an nan ya ce wa mutumin, “Miƙa hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye, kamar dai ɗayan.
14 法利赛人出去,商议怎样可以除灭耶稣。
Amma Farisiyawa suka fita suka ƙulla shawara yadda za su kashe Yesu.
15 耶稣知道了,就离开那里,有许多人跟着他。他把其中有病的人都治好了;
Da ya gane wannan, sai Yesu ya janye daga wurin. Da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da dukan masu ciwonsu,
16 又嘱咐他们,不要给他传名。
yana jan musu kunne kada su faɗa wa kowa akan ko shi wane ne.
17 这是要应验先知以赛亚的话,说:
Wannan kuwa domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya ne cewa,
18 看哪!我的仆人, 我所拣选、所亲爱、心里所喜悦的, 我要将我的灵赐给他; 他必将公理传给外邦。
“Ga bawana da na zaɓa, ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi; zan sa Ruhuna a kansa, zai kuma yi shelar adalci ga al’ummai.
19 他不争竞,不喧嚷; 街上也没有人听见他的声音。
Ba zai yi faɗa ko yă ɗaga murya ba, ba kuwa wanda zai ji muryarsa a kan tituna.
20 压伤的芦苇,他不折断; 将残的灯火,他不吹灭; 等他施行公理,叫公理得胜。
Kyauron da ya tanƙwasa ba zai karye shi ba. Fitilar da ta yi kusan mutuwa ba zai kashe ta ba, sai ya jagoranci adalci zuwa ga nasara.
21 外邦人都要仰望他的名。
Cikin sunansa al’ummai za su dogara.”
22 当下,有人将一个被鬼附着、又瞎又哑的人带到耶稣那里,耶稣就医治他,甚至那哑巴又能说话,又能看见。
Sai aka kawo masa wani bebe kuma makaho mai aljani, Yesu kuwa ya warkar da shi, har ya iya magana ya kuma sami ganin gari.
23 众人都惊奇,说:“这不是大卫的子孙吗?”
Dukan mutane suka yi mamaki, suka ce, “Wannan Ɗan Dawuda ne kuwa?”
24 但法利赛人听见,就说:“这个人赶鬼,无非是靠着鬼王别西卜啊。”
Amma da Farisiyawa suka ji haka, sai suka ce, “Ahab, da Be’elzebub sarkin aljanu ne kaɗai, wannan mutum yake fitar da aljanu.”
25 耶稣知道他们的意念,就对他们说:“凡一国自相纷争,就成为荒场;一城一家自相纷争,必站立不住;
Yesu kuwa ya san tunaninsu sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa zai lalace, kuma duk birni ko gidan da yake rabe gāba da kansa ba zai ɗore ba.
26 若撒但赶逐撒但,就是自相纷争,他的国怎能站得住呢?
In Shaiɗan yana fitar da Shaiɗan, ai, ya rabu yana gāba da kansa ke nan. Yaya kuwa mulkinsa zai ɗore?
27 我若靠着别西卜赶鬼,你们的子弟赶鬼又靠着谁呢?这样,他们就要断定你们的是非。
In kuwa ta wurin Be’elzebub nake fitar da aljanu, to, ta wa mutanenku suke fitar da su? Saboda haka, su ne za su zama alƙalanku.
28 我若靠着 神的灵赶鬼,这就是 神的国临到你们了。
Amma in ina fitar da aljanu ta wurin Ruhun Allah ne, to, fa, mulkin Allah ya zo muku ke nan.
29 人怎能进壮士家里,抢夺他的家具呢?除非先捆住那壮士,才可以抢夺他的家财。
“Ko kuwa, yaya wani zai iya shiga gidan mai ƙarfi yă ƙwace masa kaya ba tare da ya fara daure mai ƙarfin nan tukuna ba? Sa’an nan zai iya washe gidansa.
30 不与我相合的,就是敌我的;不同我收聚的,就是分散的。”
“Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni ne, kuma wanda ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi.
31 所以我告诉你们:“人一切的罪和亵渎的话都可得赦免,惟独亵渎圣灵,总不得赦免。
Saboda haka ina gaya muku, za a gafarta wa mutane kowane zunubi da kuma saɓo, amma saɓo game da Ruhu, ba za a gafarta ba.
32 凡说话干犯人子的,还可得赦免;惟独说话干犯圣灵的,今世来世总不得赦免。” (aiōn g165)
Duk wanda ya zargi Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya zargi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, ko a wannan zamani ko a zamani mai zuwa. (aiōn g165)
33 “你们或以为树好,果子也好;树坏,果子也坏;因为看果子就可以知道树。
“Itace mai kyau, yakan ba da’ya’ya masu kyau. Itace marar kyau kuma, yakan ba da’ya’ya marasa kyau. Itace dai, da irin’ya’yansa ne ake gane shi.
34 毒蛇的种类!你们既是恶人,怎能说出好话来呢?因为心里所充满的,口里就说出来。
Ku macizai, ta yaya ku da kuke mugaye za ku iya magana kirki? Gama daga baki, mutum yakan faɗi abin da yake cikin zuciya.
35 善人从他心里所存的善就发出善来;恶人从他心里所存的恶就发出恶来。
Mutumin kirki yakan fito da abubuwa masu kyau daga ajiyar da aka a yi cikinsa, mugun mutum kuwa yakan fito da mugayen abubuwa daga cikin muguntar da aka yi ajiya a cikinsa.
36 我又告诉你们,凡人所说的闲话,当审判的日子,必要句句供出来;
Amma ina gaya muku cewa mutane za su ba da lissafi a ranar shari’a a kan kowace kalmar banza da suka faɗa.
37 因为要凭你的话定你为义,也要凭你的话定你有罪。”
Gama ta wurin kalmominka za a kuɓutar da kai, kuma ta wurin kalmominka za a hukunta ka.”
38 当时,有几个文士和法利赛人对耶稣说:“夫子,我们愿意你显个神迹给我们看。”
Sa’an nan waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki suka ce masa, “Malam, muna so mu ga wata alama mai banmamaki daga gare ka.”
39 耶稣回答说:“一个邪恶淫乱的世代求看神迹,除了先知约拿的神迹以外,再没有神迹给他们看。
Sai ya amsa ya ce, “Mugaye da masu zinan zamanin nan suna neman wata alama mai banmamaki! Amma babu wadda za a nuna musu, sai dai alama ta annabi Yunana.
40 约拿三日三夜在大鱼肚腹中,人子也要这样三日三夜在地里头。
Gama kamar yadda Yunana ya yi yini uku da kuma dare uku a cikin wani babban kifi, haka Ɗan Mutum zai yi yini uku da kuma dare uku a cikin ƙasa.
41 当审判的时候,尼尼微人要起来定这世代的罪,因为尼尼微人听了约拿所传的就悔改了。看哪,在这里有一人比约拿更大!
Mutanen Ninebe za su tashi a ranar shari’a tare da wannan zamani, su kuwa hukunta shi; don sun tuba saboda wa’azin Yunana, yanzu kuwa ga wanda ya fi Yunana girma a nan.
42 当审判的时候,南方的女王要起来定这世代的罪;因为她从地极而来,要听所罗门的智慧话。看哪,在这里有一人比所罗门更大!”
Sarauniyar Sheba za tă tashi a ranar shari’a tare da wannan zamani, tă kuwa hukunta shi; don ta zo daga ƙarshen duniya, ta saurari hikimar Solomon, yanzu kuwa ga wanda ya fi Solomon girma a nan.
43 “污鬼离了人身,就在无水之地过来过去,寻求安歇之处,却寻不着。
“Sa’ad da mugun ruhu ya fita daga mutum, yakan bi wuraren da ba ruwa yana neman hutu, ba ya kuwa samu.
44 于是说:‘我要回到我所出来的屋里去。’到了,就看见里面空闲,打扫干净,修饰好了,
Sa’an nan yakan ce, ‘Zan koma gidan da na bari.’ Sa’ad da ya iso, ya tarar da gidan ba kowa a ciki, shararre, kuma a kintse.
45 便去另带了七个比自己更恶的鬼来,都进去住在那里。那人末后的景况比先前更不好了。这邪恶的世代也要如此。”
Sai yă je yă ɗebo waɗansu ruhohi bakwai da suka fi shi mugunta, su kuwa zo su shiga su zauna a can. Ƙarshen mutumin nan fa zai fi farkonsa muni. Haka zai zama ga wannan mugun zamani.”
46 耶稣还对众人说话的时候,不料他母亲和他弟兄站在外边,要与他说话。
Yayinda Yesu yake cikin magana da taron, sai ga mahaifiyarsa da’yan’uwansa tsaye a waje, suna so su yi magana da shi.
47 有人告诉他说:“看哪,你母亲和你弟兄站在外边,要与你说话。”
Wani ya ce masa, “Mahaifiyarka da’yan’uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai.”
48 他却回答那人说:“谁是我的母亲?谁是我的弟兄?”
Ya amsa masa ya ce, “Wace ce mahaifiyata, su wane ne kuma’yan’uwana?”
49 就伸手指着门徒,说:“看哪,我的母亲,我的弟兄。
Sai ya miƙa hannu wajen almajiransa ya ce, “Ga mahaifiyata da kuma’yan’uwana.
50 凡遵行我天父旨意的人,就是我的弟兄姊妹和母亲了。”
Ai, duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda yake cikin sama, shi ne ɗan’uwana da’yar’uwata da kuma mahaifiyata.”

< 马太福音 12 >