< ՅԱՅՏՆՈՒԹԻՒՆ ՅՈՎՀԱՆՆՈՒ 6 >

1 Նայեցայ՝ երբ Գառնուկը բացաւ կնիքներէն մէկը՝՝, եւ լսեցի չորս էակներէն մէկուն ձայնը՝ որոտումի պէս, որ կ՚ըսէր. «Եկո՛ւր ու տե՛ս»:
Na duba lokacin da Dan Ragon ya bude daya daga cikin hatiman bakwai, sai na ji daya daga cikin rayayyun halittattun hudu ya fada da murya kamar tsawa, ''Zo!”
2 Եւ տեսայ. ահա՛ ճերմակ ձի մը կար, որուն վրայ հեծնողը ունէր աղեղ մը: Պսակ մը տրուեցաւ անոր, ու դուրս ելաւ իբր յաղթող՝ որպէսզի յաղթէ:
Sai Na duba sai ga wani farin doki, mahayinsa na rike da baka, kuma an bashi rawani. Ya fito a matsayin mai nasara domin ya yi nasara.
3 Երբ բացաւ երկրորդ կնիքը, լսեցի երկրորդ էակը՝ որ կ՚ըսէր. «Եկո՛ւր»:
Sa'anda Dan Ragon ya bude hatimi na biyu, sai na ji rayayyen halitta na biyu ya ce, ''Zo!''
4 Ուրիշ, շառագոյն ձի մը դուրս ելաւ, եւ անոր վրայ հեծնողին իշխանութիւն տրուեցաւ՝ որ երկրէն վերցնէ խաղաղութիւնը, որպէսզի մորթեն զիրար. ու մեծ սուր մը տրուեցաւ անոր:
Sai wani doki ya fito waje - jawur. Ga mahayin aka bashi dama ya dauke salama daga duniya, domin mutanen ta su karkashe juna. Wannan mahayin an bashi babbar takobi.
5 Երբ բացաւ երրորդ կնիքը, լսեցի երրորդ էակը՝ որ կ՚ըսէր. «Եկո՛ւր ու տե՛ս»: Եւ տեսայ. ահա՛ սեւ ձի մը կար, որուն վրայ հեծնողը՝ ձեռքին մէջ ունէր կշիռք մը:
Sa'anda Dan Ragon ya bude hatimi na uku, sai na ji rayayyen halita na uku ya ce, ''Zo!'' Na ga bakin doki, mai hawanta na rike da ma'auni a cikin hannunsa.
6 Չորս էակներուն մէջէն լսեցի ձայն մը՝ որ կ՚ըսէր. «Կապիճ մը ցորենը՝ մէկ դահեկանի, ու երեք կապիճ գարին՝ մէկ դահեկանի: Մի՛ վնասեր ձէթին եւ գինիին»:
Sai na ji kamar wata murya daga cikin rayayyun halittattun nan hudu ta ce, “Mudun alkama guda a kan albashin yini, kuma mudun sha'ir uku. Amma kar ka bata mai da kuma ruwan inabi.”
7 Երբ բացաւ չորորդ կնիքը, լսեցի չորրորդ էակին ձայնը՝ որ կ՚ըսէր. «Եկո՛ւր ու տե՛ս»:
Da Dan Ragon ya bude hatimi na hudu, na ji muryar rayayyen halitta na hudu ya ce, ''Zo!''
8 Եւ տեսայ. ահա՛ տժգոյն ձի մը կար, որուն վրայ հեծնողին անունը Մահ էր, ու դժոխքը կը հետեւէր անոր: Իշխանութիւն տրուեցաւ անոնց՝ երկրի քառորդին վրայ, որ սպաննեն թուրով, սովով, մահով ու երկրի գազաններով: (Hadēs g86)
Sai na ga wani doki ruwan toka. Mai hawansa an bashi suna mutuwa, hades kuma tana biye da shi. An basu iko bisa kashi hudu na duniya su kashe da takobi, yunwa, cututtuka, da kuma namomin jeji na duniya. (Hadēs g86)
9 Երբ բացաւ հինգերորդ կնիքը, զոհասեղանին ներքեւ տեսայ անձերը անոնց՝ որ մորթուած էին Աստուծոյ խօսքին համար, եւ իրենց տուած վկայութեան համար:
Da Dan Ragon ya bude hatimi na biyar, a karkashin bagadi sai na ga rayukan wadanda aka kashe saboda maganar Allah, da kuma shaidar da suka rike.
10 Անոնք բարձրաձայն աղաղակեցին. «Սո՛ւրբ եւ ճշմարի՛տ Տիրակալ, մինչեւ ե՞րբ պիտի չդատես ու չառնես մեր արիւնին վրէժը երկրի բնակիչներէն»:
Suka yi kuka da babban murya, ''Sai yaushe ya mai iko duka, Mai Tsarki da gaskiya, zaka shari'anta mazaunan duniya, ka kuma dauki fansar jininmu?
11 Ճերմակ պարեգօտ տրուեցաւ անոնցմէ իւրաքանչիւրին, եւ ըսուեցաւ անոնց որ հանգչին քիչ մը ժամանակ ալ, մինչեւ որ ամբողջանան իրենց ծառայակիցներն ու անոնց եղբայրները՝ որոնք պիտի սպաննուէին իրենց պէս:
Sai kowanne dayan su aka bashi farar tufa aka kuma fada masu su kara jira na lokaci kadan har sai adadin abokan bautar su da kuma 'yan'uwansu maza da mata wadanda aka kashe ya cika, kamar yadda aka kashe su.
12 Տեսայ՝ երբ բացաւ վեցերորդ կնիքը, եւ ահա՛ մեծ երկրաշարժ մը եղաւ: Արեւը սեւցաւ՝ մազեղէն քուրձի մը պէս, լուսինը (բոլորովին) արիւնի գոյնի պէս եղաւ,
Da Dan Ragon ya bude hatimi na shidan, ina kallo sai ga babbar girgizar kasa. Rana ta zama baki kirin kamar bakar tufa, wata kuma ya zama kamar jini.
13 ու երկինքի աստղերը ինկան երկրի վրայ, ինչպէս սաստիկ հովէն շարժուած թզենին կը թափէ իր տհաս պտուղները:
Taurarin sama suka fado kasa, kamar yadda itacen baure ke karkade 'ya'yansa da basu nuna ba, yayin da babbar iska ta kada.
14 Երկինքը կծկուեցաւ ոլորուող մագաղաթի մը պէս, եւ բոլոր լեռներն ու կղզիները շարժեցան իրենց տեղերէն:
Sama kuma ta bace kamar takardar da aka nannade. Kowanne dutse da tsibiri aka kau da shi daga wurinsa.
15 Երկրի թագաւորները, մեծամեծները, հարուստները, հազարապետները, զօրաւորները, եւ բոլոր ստրուկներն ու բոլոր ազատները պահուըտեցան քարայրներու եւ լեռներու ժայռերուն մէջ,
Sai sarakan duniya da muhimman mutane da sarakunan yaki, attajirai, da masu iko, tare da kowanne mutum, bawa da 'yantacce suka boye cikin duwatsu da tsaunuka.
16 ու կ՚ըսէին լեռներուն եւ ժայռերուն. «Ինկէ՛ք մեր վրայ ու պահեցէ՛ք մեզ գահին վրայ բազմողին երեսէն, եւ Գառնուկին բարկութենէն:
Suka ce wa tsaunuka da duwatsu, “Ku fado bisan mu! Ku boye mu daga fuskar wanda yake zaune bisa kursiyin da kuma fushin Dan Ragon.
17 Որովհետեւ անոր բարկութեան մեծ օրը եկաւ, եւ ո՞վ կրնայ դիմանալ»:
Domin babban ranar fushin sa ta zo. Wa zai iya tsayawa?''

< ՅԱՅՏՆՈՒԹԻՒՆ ՅՈՎՀԱՆՆՈՒ 6 >