< ԳԱՂԱՏԱՑԻՍ 6 >

1 Եղբայրնե՛ր, եթէ մարդ մը որեւէ յանցանքի մէջ բռնուի, դուք որ հոգեւոր էք՝ այդպիսին հեզութեա՛ն հոգիով ուղղեցէք. ուշադի՛ր եղիր դուն քեզի, որ դո՛ւն ալ չփորձուիս:
'Yan'uwa, idan an kama mutum yana yin wani laifi, ku da kuke da ruhaniya sai ku dawo da mutumin a hanya cikin ruhun tawali'u, ka lura da kanka don kada kai ma ka fada a cikin gwaji.
2 Կրեցէ՛ք իրարու ծանրութիւնները, եւ ա՛յդպէս գործադրեցէք Քրիստոսի օրէնքը:
Ku dauki damuwar juna, ta yin haka za ku cika shari'ar Almasihu.
3 Արդարեւ եթէ մէկը՝ որ ոչի՛նչ է՝ կարծէ թէ ինք բա՛ն մըն է, ինքզինք կը խաբէ:
Domin idan kowa ya zacci shi wani abu ne alhali shi ba komai ba ne rudin kansa yake yi.
4 Բայց իւրաքանչիւրը թող քննէ իր գործը, եւ ա՛յն ատեն պարծենայ՝ միայն ինքնիր վրայ, ո՛չ թէ ուրիշի վրայ.
Sai kowa ya auna aikin sa. Sa'annan zai sami abin da zai yi takama, ba sai ya kwatanta kansa da wani ba.
5 որովհետեւ իւրաքանչիւրը պիտի կրէ ի՛ր բեռը:
Domin kowa zai dauki nauyin kayansa.
6 Խօսքին աշակերտը հաղորդակից թող ընէ իր վարդապետը ամէն բարի բանի:
Wanda aka koya masa maganar, wajibi ne ya ci amfanin abubuwansa masu kyau duka tare da malaminsa.
7 Մի՛ խաբուիք, Աստուած չի ծաղրուիր. որովհետեւ ի՛նչ որ մարդ կը սերմանէ, զա՛յն ալ պիտի հնձէ:
Kada fa a yaudare ku ba a yi wa Allah ba'a. Dukan abin da mutum ya dasa, shine abin da zai girba.
8 Ա՛ն որ իր մարմինին համար կը սերմանէ, այդ մարմինէն ապականութիւն պիտի հնձէ. իսկ ա՛ն որ Հոգիին համար կը սերմանէ, այդ Հոգիէն յաւիտենական կեանք պիտի հնձէ: (aiōnios g166)
Domin shi wanda ya shuka wa kansa dabi'ar zunubi zai girbi hallaka, amma shi wanda ya shuka cikin Ruhu, zai girbi rai madawwami daga Ruhu. (aiōnios g166)
9 Ուստի բարիք գործելէ չձանձրանա՛նք, քանի որ յատուկ ատենին պիտի հնձենք՝ եթէ չպարտասինք:
Kada mu gaji da aikata nagarta, domin a lokacin da ya dace za mu yi girbi idan ba mu gaji ba.
10 Ուրեմն, քանի պատեհութիւն ունինք, բարի՛ք ընենք բոլորին, մա՛նաւանդ՝ հաւատքի ընտանիքէն եղողներուն:
Saboda haka, lokacin da muke da zarafi, sai mu yi nagarta ga kowa. Mu yi nagarta mussamman ga wadanda suke na iyalin bangaskiya.
11 Նայեցէ՛ք, ո՛րքան մեծ գիրերով գրեցի ձեզի՝ ի՛մ ձեռքովս:
Dubi yawan wasikun da na rubuta maku da hannuna.
12 Բոլոր անոնք՝ որ կ՚ուզեն մարմինին համեմատ լաւ երեւնալ, կը հարկադրեն ձեզ որ թլփատուիք, միայն՝ որպէսզի չհալածուին Քրիստոսի խաչին համար:
Wadanda suke so su nuna hali mai kyau cikin jiki suke tilasta ku yin kaciya. Suna yin haka ne kadai saboda kada a tsananta masu saboda gicciyen Almasihu.
13 Արդարեւ ո՛չ իսկ իրե՛նք՝ թլփատուածները կը պահեն Օրէնքը. բայց կ՚ուզեն որ դուք թլփատուիք, որպէսզի պարծենան ձեր մարմինով:
Domin ko su wadanda suke masu kaciya ba su kiyaye shari'a. Maimakon haka suna so ne a yi maku kaciya don su yi fahariya game jikinku.
14 Բայց ես ամե՛նեւին պիտի չպարծենամ, այլ միայն մեր Տէրոջ՝ Յիսուս Քրիստոսի խաչով. անով աշխարհը խաչուած է ինծի համար, ես ալ՝ աշխարհի:
Bari kada ya zama ina fahariya sai dai ta gicciyen Ubangijinmu Yesu Almasihu. Ta wurinsa ne aka gicciye duniya a gare ni, ni kuma ga duniya.
15 Որովհետեւ Քրիստոս Յիսուսով ո՛չ թլփատութիւնը որեւէ ազդեցութիւն ունի, ո՛չ անթլփատութիւնը, հապա՝ նոր արարած ըլլալը:
Domin kaciya ko rashin kaciya ba komai ba ne. Maimakon haka, sabon halita ne ke da muhimmanci.
16 Խաղաղութիւն ու ողորմութիւն բոլոր անոնց վրայ՝ որ այս կանոնին համաձայն կ՚ընթանան, եւ Աստուծոյ Իսրայէլին վրայ:
Ga dukan wadanda za su zauna cikin wannan ka'ida, bari salama da jinkai su kasance tare da su da kuma bisa Isra'ila na Allah.
17 Ասկէ ետք ո՛չ մէկը թող անհանգստացնէ զիս. որովհետեւ ես մարմինիս վրայ կը կրեմ Տէր Յիսուսի վէրքին սպիները:
Daga yanzu zuwa nan gaba kada wani ya dame ni, domin ina dauke da tabbai na Yesu a jikina.
18 Եղբայրնե՛ր, մեր Տէրոջ՝ Յիսուս Քրիստոսի շնորհքը ձեր հոգիին հետ: Ամէն:
Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu ya kasance da ruhun ku, 'yan'uwa. Amin.

< ԳԱՂԱՏԱՑԻՍ 6 >