< Katwa Nono Katwa 13 >

1 Nene nanya ligozi na kagbirin Antakiya, anan liru nin nnu Kutelle nin nanan dursuzu yita ku. Tisa mine wa di Barnaba, Simeon (na iwa yicughe Niger), Lukiyus unitin Karita, Manain (unan liwalin gwanan Hiridus kukune me), nin Shawulu.
A ikkilisiyar da take a Antiyok akwai waɗansu annabawa da malamai. Barnabas, Siman wanda ake kira Baƙi, Lusiyus mutumin Sairin, Manayen (wanda aka goya tare da Hiridus mai mulki), da kuma Shawulu.
2 Kube na ndin zazinu Kutelle nin sun kotu nayi, Uruhu Ulau woro, “Feren ni Barnabas ku nin Shawulu, isu katwa kanga na nna yicila nani bara kanin.”
Yayinda suna cikin sujada da azumi ga Ubangiji, Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ku keɓe mini Barnabas da Shawulu domin aikin da na kira su.”
3 Na ligozen mmala ukotu nayi nin lira, i wunno nani likoot inin tarrda nani acara.
Saboda haka bayan suka yi azumi da addu’a, sai suka ɗibiya musu hannuwansu a kansu suka sallame su.
4 Ame Barnabas nin Shawulu suu ubiyayya nin Ruhu Ulau itunna i nyi udu kusarin kilikiya; unuzu kikane idi tunun udu nlong lidan nanya kurawan kubrus.
Sai su biyu da Ruhu Mai Tsarki ya aika suka gangara zuwa Selusiya suka shiga jirgin ruwa daga can zuwa Saifurus.
5 Kubi na iwa di nanya kagbir salamis, ibelle uliru Kutelle nanya kutyi nlirag, na Yahudawa, inung tutun yita nan Yohanna Markus nafo unan buunu mine.
Da suka isa Salamis, sai suka yi shelar maganar Allah a majami’un Yahudawa. Yohanna yana tare da su a matsayin mai taimakonsu.
6 Kubi na inya udu vat lidan kiyitik nmyen, udu Bafusa, idi se umong unan nizu tikanlang, ku Yahudawa, unan su kinu nin nnu Kutelle, ulenge na lisa me Bar Yesu.
Suka zaga dukan tsibirin har sai da suka kai Bafos. A can suka sadu da wani mutumin Yahuda mai sihiri, annabin ƙarya, mai suna Bar-Yesu,
7 Unan nizu tikankane munu liti min mukadas, Sargis, nin Bulus unit ujinjin, unit une wasu manyardang nin Barnabas a Bulus, bara adinin su alanzauliru Kutelle.
wanda yake ma’aikacin muƙaddas Sergiyus Bulus ne. Muƙaddas ɗin kuwa mai azanci ne ƙwarai, ya sa aka kira Barnabas da Shawulu don yana so ya ji maganar Allah.
8 Ame Alima unan “nizu tikankang” (nanere lisa me di) asu ivira nanghinu, asa likum nworu a kpiliya Sarijiyus ku nanya nyinnu sa uyenu me.
Amma Elimas mai sihirin nan (domin ma’anar sunansa ke nan) ya yi hamayya da maganarsu ya kuma yi ƙoƙari ya juyar da muƙaddas ɗin daga bangaskiya.
9 Ame Shawulu, ulenge na idin yicu Bulus, awa kullun nin Ruhu Ulau a borioghe iyizi
Sai Shawulu, wanda kuma ake kira Bulus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya kafa wa Elimas ido ya ce,
10 anin woro, “Fe gono shaitan, ukulun nin kinu a karusuzo, nin magunta, fe unan nivira nin vat ko iiyeme imon icine, na uba sunu ukpilizu nimon idert in Cikilari ba sa iba sunu?
“Kai ɗan Iblis ne abokin gāban dukan abin da yake daidai! Kana cike da kowane irin ruɗi da munafunci. Ba za ka daina karkata hanyoyin da suke daidai na Ubangiji ba?
11 Nene yene ucara Cikilari di kitene fe, uba da lawu uduu. na iba yenu uwui ba nin kubi baat.” Dedei luwutun nin nsirti, a cizina kiti, intiri nanut ikifo ghe ucara.
Ga shi hannun Ubangiji yana gāba da kai. Za ka makance, kuma ba za ka ga rana ba har na wani lokaci.” Nan take, hazo da duhu suka sauko a kansa, ya yi ta lallubawa, yana neman wanda zai yi masa jagora.
12 Kubi na ame Sarjisu nyene ile imon na idi, ame yinna, bara awa kifo unuu nin ndursuzu kitene Cikilari.
Sa’ad da muƙaddas ɗin ya ga abin da ya faru, sai ya ba da gaskiya, gama ya yi mamaki a kan da koyarwa game Ubangiji.
13 Nene Bulus nan nadondon me, kaffina unuzu Bafus udu Perga nanya Pamfiliya, ame Yohanna suuna nai a kpila Urushelima.
Bulus da abokan tafiyarsa suka tashi daga Bafos a jirgin ruwa zuwa Ferga a Famfiliya inda Yohanna ya bar su ya koma Urushalima.
14 Bulus nan nadondon me, cinna unuzu Bafos udak Antakiya Nbisidiya. Kikane inya udu kutyi nlirag liyiri nassabar idi soo kikane.
Daga Ferga kuwa suka ci gaba zuwa Antiyok na Fisidiya. A ranar Asabbaci sai suka shiga majami’a suka zauna.
15 Kubi na ibelle inyerte nduka, nin na nan nliru nin nnu Kutelle, udia kutyi nlirag too nani nin kadura a woro, “Linuana, andi idinin nkan kadura, kan kpinu nagang kiti nanite kikane, bellen kanin.”
Bayan an yi karatu daga cikin Doka, da kuma Annabawa, sai shugabannin majami’ar suka aika musu suka ce, “’Yan’uwa, in kuna da wani saƙon ƙarfafawa domin jama’a, sai ku yi.”
16 Bara Bulus fita ayisina a zillino liti me, a woro, “Annit Israila nin nalenge na idin zazinu Kutelle, lanzan.
Yana miƙewa tsaye, sai Bulus ya yi musu alama da hannu ya ce, “Mutanen Isra’ila da kuma ku Al’ummai da kuke wa Allah sujada, ku saurare ni!
17 Kutelle nanit ale Israila wa feer acif bite ata nani anit gbardang, kubi na iwa so nmyin masar, nin nacara nakara awa nutun nani kitee.
Allahn mutanen Isra’ila ya zaɓi kakanninmu; ya kuma sa mutanen suka yi bunkasa yayinda suke zama a ƙasar Masar, da iko mai girma ya fitar da su daga ƙasar,
18 Udu akus akut anas, ayita nanghinu nanya kusho.
ya kuma jure da halinsu har shekara arba’in a cikin hamada,
19 Kubi na awa mallu nin nipin kuzor, nanyan nmyin kaana, anaa anit bite nmyin mine miso nani ugadu.
ya tumɓuke ƙasashe bakwai a Kan’ana ya kuma ba da ƙasarsu gādo ga mutanensa.
20 Vat nile imone iwasu inin ukatu nakus akalt anas nin nakut ataun, kubi nile imone vat, Kutelle na nani unan wucu kidegen udu Samaila unan nliru nin nnu Kutelle.
Dukan wannan ya ɗauki kusan shekaru 450. “Bayan wannan, Allah ya ba su alƙalai har zuwa zamanin annabi Sama’ila.
21 Mammal nilele, anite tirino ini nani ugo, Kutelle na nani Saul ku usaun kish, unit unuzu likuran Banyami, bara kubi nakus akut annas.
Sa’an nan mutanen suka nemi a ba su sarki, Allah kuwa ya ba su Shawulu ɗan Kish, na kabilar Benyamin, wanda ya yi mulki shekaru arba’in.
22 Na kutelle nkalaghe nanya nanan tigo, a yauna Dauda ku aso nani ugo, uwaso kitene Dauda kutelle wa woro, 'Nnase Dauda usaun Jesse aso unit nayi nighe; aba su vat nile imon na ndinin su we.'
Bayan an kau da Shawulu, sai ya naɗa Dawuda ya zama sarkinsu. Ya kuma yi shaida game da shi cewa, ‘Na sami Dawuda ɗan Yesse, mutum ne da nake so a zuciyata; shi zai aikata dukan abin da nake so.’
23 Unuzu kuwunu nnit ule Kutelle ba da ni nonon Israila ku unan tucu, Yesu nafo na anusu alikawali nsu we.
“Daga zuriyar mutumin nan ne Allah ya kawo wa Isra’ila Mai Ceto Yesu, kamar yadda ya yi alkawari.
24 Uleli imone wa cizin kube, kamin Yesu dak, Yohanna wa cizin ubellun nshimtinnu ndiu kutyin, udu kiti nanit Israila vat.
Kafin zuwan Yesu, Yohanna ya yi wa’azin tuba da baftisma ga dukan mutanen Isra’ila.
25 Na Yohanna wadi malizunu katuwa me, aworo, 'Anung din su meng ghari? Na mere ba, ama lanzan, umong din cinu udak kidung nighe, akwatak nabunu me na meng batin nbunku ba.'
Yayinda Yohanna yake kammala aikinsa ya ce, ‘Wa kuke tsammani ni nake? Ba ni ne shi ba. A’a, amma yana zuwa bayana, wanda ko takalmansa ma ban isa in kunce ba.’
26 Linuana, nono nanya kuwunu Ibrahim, nin nanya mine na idin dortu Kutelle, kiti bitere, kadura nbellen nnan tucu iwa tuu nari mun.
“Ya ku’yan’uwa,’ya’yan Ibrahim, da ku kuma Al’ummai masu tsoron Allah, a gare mu ne fa aka aiko wannan saƙon ceto.
27 Bara inughe na iwa sosin nanyan Urushelima nan nago mine, na iwa yinin ghe ba, sa iyinin tiwui nanan nliru nnu Kutelle na isa ibelle ko ayeme assabar, ina ni na Kullo ubellu we, kadure nti Yesu unan kul.
Mutanen Urushalima da masu mulkinsu ba su gane da Yesu ba, duk da haka cikin hukunta shi suka cika kalmomin annabawan da ake karantawa kowane Asabbaci.
28 Vat nani na iwase imomon icaut kiti me nworu akuu ba, itirino Bilatus ku nworu amollu ghe.
Ko da yake ba su same shi da wani dalilin da ya kai ga hukuncin kisa ba, suka roƙi Bilatus yă sa a kashe shi.
29 Kubi na imala vat nile imon na ina nyertu liti me itoltunghe kitene kutca, inonko ghe nanya kissek.
Sa’ad da suka aikata duk abin da aka rubuta game da shi, sai suka saukar da shi daga itacen suka kuma sa shi a kabari.
30 Amma Kutelle wa fya ghe nanya na nan kul.
Amma Allah ya tashe shi daga matattu,
31 Anit gbardang wa yenje ghe nanya nayiri gbardang na lenge na i di ligowe nan ghe na i wa nuzun Galile ne indu Urushelima. Anit alelere iyizi naba me kiti nanite.
kuma kwanaki da yawa waɗanda suka yi tafiya tare da shi daga Galili zuwa Urushalima suka gan shi. Su ne yanzu shaidu ga mutanenmu.
32 Bara nani ti da minu nin liru unang imbeleng nciu nnuu ulenge na iwa su an kaa bite unin uworsu:
“Muna gaya muku labari mai daɗi cewa abin da Allah ya yi wa kakanninmu alkawari,
33 Kutelle na ceo nari uciu nlirne, arik nono mine, nworu Kutelle wa fya Yesu ku kisssek.
ya cika mana, mu zuriyarsu, ta wurin tā da Yesu daga matattu. Kamar yadda yake a rubuce a cikin Zabura ta biyu cewa, “‘Kai Ɗana ne, yau na zama Uba a gare ka.’
34 Ununu kidegen nworu ana fya ghe nanya na nan kul bara kidowo me wa yene ubiju, amini wa su uliru nenge, 'Mma nifi nkoli milau in nanda milau.'
Gaskiyar cewa Allah ya tā da shi daga matattu, a kan ba zai taɓa ruɓewa ba, an faɗe shi a cikin waɗannan kalmomi. “‘Zan ba ku tsarki da kuma tabbatattun albarkun da na yi wa Dawuda alkawari.’
35 Unnare nati ana kuru abelle nan nya namong avu tutung: 'Na una yinnu unit ulau fe a yene ubiju ba.'
Haka kuma aka faɗa a wani wuri. “‘Ba za ka yarda Mai Tsarkinka ya ruɓa ba.’
36 Bara na kimal na Dauda wa su Kutelle katwa kubi kiyi mine gegeme kanin aku. iwa aoroghe nin na cif me, amini wa biju,
“Gama sa’ad da Dawuda ya gama hidimar nufin Allah a zamaninsa, sai ya yi barci; aka binne shi tare da kakanninsa jikinsa kuwa ya ruɓe.
37 amma ame ulenge na Kutelle wa fya Kissek na awa yene ubiju ba.
Amma wanda Allah ya tā da daga matattu bai ruɓa ba.
38 Linuana na iyinnin ilele, unuzu nlele ina sun nari unuu nbeleng nkussu nalapi.
“Saboda haka,’yan’uwana, ina so ku san cewa ta wurin Yesu ana sanar muku da gafarar zunubi.
39 Bara ame vat ule na ayinni ma se usurtu nan nye vat ule na ti tisse usurtu mun ba.
Ta wurinsa kowa da ya gaskata an kuɓutar da shi daga dukan abin da Dokar Musa ba tă iya kuɓutar ba.
40 Bara ceon nibinai kiti kirum bara imon ile na a annabawa na belin kitene i wa minu ba.
Ku lura kada abubuwan da annabawa suka faɗa su faru muku.
41 Yeneng, anung anan nanzu nimon nafi fiu kifo minu inana. Bara meng din su katwa nayiri mine, Katwaa kango na ima yinnu mun ba andi ma umong ma belin minu ubeleng kanin.'”
“‘Ku duba, ku masu ba’a, ku yi mamaki, ku hallaka, gama zan yi wani abu a zamaninku da ba za ku taɓa gaskatawa ba ko da wani ya gaya muku.’”
42 Na Bulus nin Barnabas nnyaa, anite fo nani acara nworu ikuru ida belu nani uliru urum une Asabar ncin dak.
Bulus da Barnabas suna fita daga majami’ar ke nan, sai mutane suka gayyace su su ƙara yin maganan nan a kan waɗannan abubuwa a ranar Asabbaci mai zuwa.
43 Na uzuru kilari nlire nmala, Ayahudawa gbardang nin namon anan salin dortu Kutelle dofino Bulus ku nin Barnabas, alenge na iwa su nani uliru i woro nani ili ubun nin cin nan nya nbolu Kutelle.
Da aka sallami jama’a, Yahudawa da yawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci masu ibada suka bi Bulus da Barnabas, waɗanda suka yi magana musu suka kuma ƙarfafa su su ci gaba a cikin alherin Allah.
44 Assabar nda duru anan kagbiri vat da zuro inan lanza uliru Ncikilari.
A ranar Asabbaci na biye kusan dukan birnin suka taru don su ji maganar Ubangiji.
45 Na Ayahudawa in yene ligozi nanite, ikulo nin shina isu uliru uganbalang nin nilenge na Bulus nbelle izoguzo ghe.
Sa’ad da Yahudawa suka ga taron mutanen, sai suka cika da kishi suka yi ta munanan maganganu a kan abin da Bulus yake faɗi.
46 Amma Bulus nin Barnabas su uliru nin nayi akone i woro, “Uso gbas i cizin ubelu anughe ku uliru Kutelle. Na iyene nworu anung nfillo unin ina nin yira ati mine na ucaun ise ulai nsa ligan ba, yeneng, tima kpillu kiti na wurmi. (aiōnios g166)
Sai Bulus da Barnabas suka amsa musu gabagadi, suka ce, “Ya zama mana dole mu yi muku maganar Allah da farko. Da yake kun ƙi ta ba ku kuma ga kun cancanci rai madawwami ba, to, za mu juya ga Al’ummai. (aiōnios g166)
47 Bara nanere Cikilari na bellin nari, aworo, 'Nna ceo minu nafo nkanan ucin du kiti na wurmi, nworo adak nin adak nin tucu nan nyan vat niti nan nya in yii vat'”
Gama abin da Allah ya umarce mu ke nan cewa, “‘Na sa ka zama haske ga Al’ummai, don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya.’”
48 Na Awurme nlanza nani, ilanza mmang kang izazina lissa Ncikilari. Ngbardang nalenge na ina fere nani bara ulai nsa ligang wa yinnin. (aiōnios g166)
Sa’ad da Al’ummai suka ji haka, sai suka yi farin ciki suka ɗaukaka maganar Ubangiji; kuma duk waɗanda aka zaɓa don samun rai madawwami, suka gaskata. (aiōnios g166)
49 Uliru Kutelle wa malu kiti vat nan nya nmine.
Maganar Ubangiji kuwa ta bazu a dukan yankin.
50 Amma Ayahudawa su ubeleng nawani anan ni nati alenge na idi nin nimon icine. Ileli imon ta nworu ipiziru umonlun Bulus ku nin Barnabas iko nani inutuno nani unuzu kipin mine.
Amma Yahudawa suka zuga waɗansu mata masu tsoron Allah masu martaba da kuma waɗansu maza masu matsayi a gari. Suka tā da tsanani ga Bulus da Barnabas, suka kore su daga yankinsu.
51 Amma Bulus nin Barnabas kotuno lidau nabunu mine liso nati mine. Inya ucindu kipin Ikoniya.
Saboda haka suka karkaɗe ƙurar ƙafafunsu don shaidar a kansu suka kuwa tafi Ikoniyum.
52 Nono kadura wa kulo nin nayi abo a Uruhu Ulau.
Masu bi kuwa suka cika da farin ciki da kuma Ruhu Mai Tsarki.

< Katwa Nono Katwa 13 >